Coronavirus: Limamin Katolika ya yi iƙirarin gano maganin cutar

An wallafa

Babban limamin cocin Katolika na birnin Duala da ke Jamhuriyar Kamaru, Samuel Clade, ya yi ikirarin cewa yana da maganin gargajiya da zai warkar da cutar korona.

Sai dai maganin da limamin cocin ya fito da shi ya fuskaci suka daga likitocin kasar wadanda suka ce ba a gwada shi ba.

Ya ce duk da cewa bai bai wa maganin nasa suna ba, ya yi wa 'yan kasar alkawarin cewa zai fito da maganin kyauta ga jama'a

Samuel Claude ya ce za a samu maganin a asibitocin darikar Katolika ne a wasu birane da ke jamhuriyar.

Dangane kuma na sukar maganin nasa da kungiyar likitocin Kamaru ta yi, Samuel Claude ya ce "ruwansu ko su aminta da maganina ko su yi watsi da shi, ni dai zan fito da shi. Ba za mu bari jama'a su yi ta mutuwa ba."

Zakuwa da jama'ar kasar suka yi na jiran wannan magani ne ya sa wasu tuni suka fito da wani magani mai dauke da sunan Samuel Claude domin sayar wa jama'a.

Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta sha yin gargadi da jama'a su guji amfani da magungunan gargajiyar da masana da likitoci ba su amince da shi ba sakamakon rashin yin gwaji.

Pastor Samuel Claude ne ba shi ne mutum na farko da ya yi ikirarin gano maganin cutar korona a Afirka ba.

Ko a 'yan makonnin da suka gabata sai da shugaban kasar Madagascar, Andry Rajoelina ya ce maganin gargajiya na tazargade na maganin cutar korona.