Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za mu hukunta duk wanda ya tsallaka iyakar Najeriya ba da izini ba'
Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta gargadi al'ummomin kasashen da ke da iyaka da kasar da su guji zirga-zirga a tsakanin kasashen da Najeriya.
Hukumar ta jadada gargadinta da sake tunasar da cewa kasar ta rufe iyakokin ta na kasa da na sama domin shawo kan annobar cutar ckrona, a saboda haka ne ta ce duk wanda ya taka wannan doka zai fuskanci hukuncin shari'a.
Shugaban hukumar Muhammed Babandede, ya shaida wa BBC cewa yakamata jama'a su sani cewa wannan annoba cuta ce da ake yadawa tsakanin mutum da mutum, don haka tun da gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta na kasa da na samu to bai kamata a rinka tsallaka iyakokin ba tare da sanin hukuma ba.
Ya ce "Abin da ke faruwa tun da aka rufe iyakokin kasar muna karbar 'yan Najeriya ne kadai wanda suke dawowa gida don ba wanda ya isa ya hana dan Najeriya dawowa gida".
Babandede, ya ce " To suma din idan sun shigo cikin kasar dole ne hukuma ta sani sannan a bada su wajen hukumar lafiya saboda a tabbatar mutanen nan an killacesu har kwana goma sha hudu kafin su shiga al'umma".
Ya ce, yakamata mutanen da ke zaune a iyakokin Najeriya su dauki wannan abu da muhimmanci, don ba za a lamunci mutane su rinka tsallakawa iyaka ba tare da sanin hukuma ba.
Babandede, ya ce, wannan doka ce kuma duk wanda ya karyata zai fuskanci hukuncin kuliya.
Ya ce " Dama can akwai wannan dokar ba wai don cutar korona ba, akwai dokar gwamnati da ta ce duk wanda ya shiga Najeriya ba tare da sanin hukuma ba idan aka kama shi za a hukunta shi".
Shugaban hukumar shige da ficen ya ce a dokarsu ta 'Immigration act' duk wani mutum da ya shigo ko ya fita daga Najeriya ba tare da ya mika kansa ga hukumar shige da fice ba, to za a iya hukunta shi idan an kai shi gaban alkali wand zai iya yi masa hukunci daurin shekara daya ko biyu ko kuma ya biya tara.
Babandede, ya ce " A don haka wannan doka ba sabuwa bace illa mu tabbatar ana amfani da ita".