Yara na kamuwa da wata sabuwar cuta dalilin cutar korona

File photo dated 13/10/15 of a child with a carer.

Asalin hoton, PA Media

An wallafa

Gwamman yara a Amurka da Burtaniya ne suka kamu da wata cuta da ba a saba ganinta ba, kuma wadda ke da alaka da cutar korona.

A wasu daga cikin yaran, cutar na sa su a cikin mawuyacin hali inda har sai an bai wa wasu daga cikinsu kulawa ta musamman.

Yara kusan 100 ne a Burtaniya suka kamu kuma bincike ya nuna cewa an samu irin haka a wasu wuraren a Turai.

Akwai yiwuwar cewa tsaikon da ake samu kafin garkuwar jiki ta yaki cutar korona ne ke haifar da cutar da ake kira Kawasaki Shock Syndrome.

A watan Afrilu, an gaya wa likitoci a Burtaniya su sa ido kan wani mummunan martani da jiki ke mayarwa a yara.

Sabon Abu

Children playing on a beach

Asalin hoton, Getty Images

Dukkansu na da alamomi masu kama lokacin da aka kwantar da su a asibitin yara na Evelina London, ciki har da zazzabi mai zafi da kuraje da rikidewar launin ido zuwa ja, da kumburi da ciwon jiki.

Mafi yawan yaran ba su da matsalar sarkewar numfashi, duk da cewa bakwai daga cikinsu sun yi amfani da na'urar iska ta ventilator don taimaka wa zuciyarsu da gudanar jini.

Likitoci na bayyana cutar a matsayin wani "sabon abu" mai kama da cutar Kawasaki - wata cuta da ba a saba ganinta ba da ke shafar yara 'yan kasa da shekara biyar.

Alamominta sun hada da kuraje da kaluluwa a wuya da bushewa da tsagewar lebba.

Sai dai wannan sabuwar cutar na shafar har da yaran da suka fara tasawa har zuwa shekara 16, kuma kadan daga cikinsu na shioga mawuyacin hali.

Dakta Liz whittaker, wata malama da ke koyar da cutuka masu yaduwa a kananan yara a Kwalejin Imperial da ke Landan, ta ce tunda har cutar ta bayyana a tsakiyar annoba, hakan na nufin biyun suna da alaka.

"Ga wannan annobar ta Covid-19 tana tsaka da ci, kuma bayan mako uku zuwa hudu sai wannan sabuwar cutar ta bullo, muna tunanin wannan sabuwar cuta ce ta bayan annoba," a cewarta.

Wannan na nufin akwai yiwuwar cutar na da alaka da yawan kwayoyin jini na antibodies da ke yaki da cuta.

'Ba a saba ganin ta ba'

Boy being treated by a nurse

Asalin hoton, Getty Images

Farfesa Russell Viner, shugaban Kwalejin Royal a bangaren lafiyar yara y ace magani ya yi aiki kan mafi yawan yaran da suka kamu da wannan cutar kuma suna samun sauki har ma an fara sallamarsu daga asibiti.

Cuta ce da ba a saba ganin irinta ba, a cewarsa.

"Kada wannan ya hana iyaye barin 'ya'yansu fita idan an cire dokar kulle," in ji Farfesa Viner.

Ya ce fahimtar yadda cutar ta ke "na iya nuni ga yadda wasu yara suka wahala bayan kamuwa da Covid-19, yayin da mafi yawansu bas u kamu ba ko kuma bas u ji alamominta ba".

Ana tunanin yara ne kasha 1-2 cikin 100 na duka wadanda suka kamu da cutar korona a Burtaniya, kuma kasa da 500 daga cikinsu ne aka kwantar a asibiti.

Michael Levin, farfesa a bangaren lafiyar yara a Kwalejin Imperial ya yi bayanin cewa mafi yawan yara bas u kamu da cutar korona ba amma an gano kwayoyin jinni na antibodies a jikinsu.

"Don haka muna tunanin yanayin cutar ya kunshi yadda garkuwar jiki ke aiki tukuru ta yi yaki da cutar fiye da yadda ta saba," a cewarsa.

Sai dai farfesa Levin y ace "akwai sauran abubuwa da dama da za a gano" dangane da wannan cuta, wadda duka-duka makonni biyu zuwa uku da suka wuce aka gano ta.

An gano cewa cutar na shafar yara kusan makonni shidda bayan sun kamu da cutar korona, kuma hakan ya nuna bayyanara sabuwar cutar makonni da yawa bayan cutar korona ta kai kololuwarta a Burtaniya.

Girl being examined at a hospital

Asalin hoton, Getty Images

Ya lamarin yake a sauran sassan duniya?

An ga afkuwar irin haka a Amurka da Sifaniya da Italiya da Faransa da Holland.

A kalla jihohin Amurka 15 na duba cutar da ba a saba ganinta ba a cewa Gwamnan birnin New York Andrew Cuomo.

Cikin yara 82 da aka gano suna da cutar ta kumburi a New York, yara 53 ne suke dauke da cutar korona ko kuma suke da kwayoyin antibodies da ke yakar Covid-19.

Hukumar da ke kula da yaduwar cutuka ta Amurka za ta fara fitar da gargadi da cikakken bayani kan cutar ga ma'aikatan lafiya a wannan makon.

A halin da ake ciki, a cewar wani bincike da likitoci a arewacin Italiya suka yi, yara 10 ne cutar ta shafa.

Boy sitting at a table

Asalin hoton, Getty Images

Duka yara 10 da aka yi binciken a kansu sun kwanta a wani asibiti a Bergamo - birnin da ya zama cibiyar annobar a Italiya - tsakanin tsakiyar watan Fabrairu da tsakiyar watan Afrilu, kuma sun warke.

Yaran, sun samu alamomin cutar sosai kamar ciwon zuciya da alamomin wani ciwo da ke faruwa bayan tiyata wanda ke rubar da sassan jiki.

Da aka yi wa yaran gwajin kwayoyin antibody, an gano cewa 8 sun yi korona yayin da sauran biyun ba su yi ba. Amma masu binciken sun ce gwajin ba ya bayar da sahihin sakamako dari bisa dari.

Ana tunanin gwajin da ake yi ta hanyar daukar yawu da majina don gano kwayar cutar korona ba shi da tasiri saboda ita wannan sabuwar cutar ana yin ta ne makonni da dama bayan kamuwa da cutar korona.