Coronavirus: Gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar kulle

Ganduje

Asalin hoton, KNSG

An wallafa

Gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar kulle da gwamnatin tarayya ta sanya wa jihar na mako biyu.

Yanzu haka Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kara mako guda kan makonni da gwamnatin tarayyar ta sanya da manufar ganin cutar korona ba ta yadu a jihar ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya ce an cimma matsayar tsawaita dokar ne tsakanin jami'an gwamnatin tarayya da na jiha da ma kwararru kan harkar lafiya.

A wata sanarwa, Malam Muhamamd Garba ya kara da cewa "gwamnati na sane da irin radadin da jama'a ke ji sakamakon dokar kullen amma muna jan hankalin jama'a da su kwantar da hankalinsu domin gwamnatin na kokarin ganin ta takaita yaduwar wannan cuta."

Tsawaita lokacin dai na zuwa ne kwana daya bayan da wa'adin mako biyu da gwamnatin tarayyar kasar ta sanya wa jihar ta Kano ke karewa.

A ranar Litinin ne dai gwamna Ganduje ya sanar da kaddamar da shirin raba takunkumin fuska ga 'yan jihar, wanda hakan ke nufin bayan dokar kullen, sanya takunkumin ne zai zama wajibi.

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kanon dai sun kai 666, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar.