Coronavirus: Masu cutar a Legas ka iya kai wa 120,000

Asalin hoton, Twitter
Gwamnatin jihar Legas ta ce masu dauke da korona za su iya kai wa 120,000 lokacin da cutar za ta kai makurarta a tsakanin watannin Yuni da Agusta.
Kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi ne ya bayyana haka a ranar Juma'a lokacin da yake bayani ga manema labarai, yana cewa da "yiyuwar a samu mutum 90,000 zuwa 120,000 masu dauke da cutar a wannan lokacin."
Kwamishinan ya kara da cewa wannan adadin hasashe ne kawai, amma bai zama dole yawan masu dauke da cutar ya kai haka ba a jihar.
"Wata guda baya, daga ranar 7 ga watan Afirilu mun rika samu masu cutar korona 10 a ko wacce rana, mako biyu bayan nan sai adadin ya karu zuwa 32, daga nan sai 70. Yanzu kuma mutum 100 a ke samu a kowacce rana. wannan na nuna karuwar wadanda ke dauke da korona a jiharmu nan da nan.
"Mun tabbatar da cewa annobar ba ta kai makurarta ba, muna tsammanin cutar za ta kai makura ne tsakanin watannin yuni da Agusta, to dan haka dole mu shirya wa wannan tashin hankali da muke tunkara, muna kara bunkasa karfinmu da dabarun yadda muke tunkarar wannan yanayi,"
A shirin tun karar lokacin da za ta kure, Kwamishinan ya ce, jihar ta hade wasu cibiyoyin karbar samfuri wuri daya domin kara hanzari wajen murkushe annobar.
Mista Abayomi ya ce ya zuwa juma'a jihar na da mutum 1,491 da ke dauke da cutar, ba dan dabarun da ake amfani da su ba da yanzu adadin yakai 6,000.










