Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Za mu tarar da ofisoshinmu lafiya kalau kuwa idan muka koma aiki?
- Marubuci, Jane Wakefield
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology reporter
- An wallafa
Yayin da aka fara sassauta dokar zaman gida a wasu kasashen, an fara tunanin rashin tabbas kan yadda za a koma aiki, mutane na son fahimtar amincin ofishohinsu in an koma, lokacin da ake tsaka da fama da wannan annobar ta duniya.
Baya ga wasu abincin da suka fara hunhuna a firjin ofis-ofis, akwai bukatar karin na'urori da za su taimaka wajen sanya ido kan ma'aikata.
Kama daga na'urar da ke daukar bayanan zafin jikin mutum kafin shiga ofis, zuwa wadda za ta shaida maka idon ka kusanci abokin aikinka, ka wuce tazarar da ya kamata ka bayar, kwanan nan aiki zai zama tamkar wani rahohoton bibiyar yadda ake shirya fina-finai.
Shekaru kadan da suka gabata, an zabi ginin ofishin Edge da ke birnin Amsterdam a matsayin daya daga cikin gine-ginen zamani da suka samar da fasahar da ake bukata, tare da samar da tsarin shiga ofishi ta hanyar gane kwayoyin halittar jikin dan adam, sabo da kauce wa cutakan da ke barazana ga rayuwar mutane.
Coen van Oostrom shi ne shugaban kamfanin real estate wanda ya gina Edge, ya shaida wa BBC akwai 'yan sauye-sauye da ke zuwa cikin gaggawa wadanda "ba ka tsara aikin da su ba".
Ingattaciyar iska
"Ana iya bude kofofi da hannu, amma akwai 'yan sauye-sauye na yadda zaka iya bude kofar da muryarka ta hanyar wata manhaja, muna yin hakan ne domin tabbatar da cutar ba ta yaduwa ta wannan hanyar.
Kuma muna da kyamarorin da kan iya ganin mutane nawa ne a hawa, akwai manhajar da zata ba da damar gane tazarar da ke tsakanin ko wanne mutum, idon mutane suka kusanci juna sosai, za mu rika tura musu sakon gargadi ta wayoyinsu cewa su ba da tazara.
"Ba kowa ne ke son hakan ba, da yawa na cewa wannan kamar kutse ne cikin sirrikansu, to dan haka har yanzu ba mu gama yanke shawarar ko za mu yi amfani da fasahar ba lokacin da kowa ya dawo aiki."
Ginin Edge ba kamar kowanne gini yake ba, tuni ya samar wa ma'aikata wata manhajar wayar hannu da zata basu damar ganin yawan zafin ofis, wacce irin ingattaciyar iska ce a ciki, kuma zai basu damar siyan abinci daga inda suke.
Har yanzu bai samu wata gagarumar karbuwa ba. Wanda a baya babu wanda ya damu da inganci iskar da yake shaka, akwai yiyuwar yaduwar cutar idon babu ingattaciyar iska da ke kai komo, mutane sun fara damuwa da ita, a ganin Mista van Oostrom.
Sauya tsarin zaman ofis da tabbatar da ana ba da tazara tsakanin mutane shi ne abin da ya kamata, amma Susan Clarke wata kwararriya a harkokin ginin zamani da ke aiki da kamfanin Verdantix, na ganin abu ne mawuyaci kamfanoni da ofis-ofis su sauya tsarin yadda suke gudanar da ayyukansu.
"Samun wajen zaman dinidindin a ofis zai ci gaba da kasancewa, kuma ganin irin matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta yanzu, mafi yawan ofisoshi ba za su kara fadada wurarensu ba - amma za a iya sake tunani a kai, da wani ya gama aiki da teburin da yake kai sai a kira masu shara su fesa magnin kashe kwayoyin cuta, wani ya ci gaba da aiki a wurin."
Wasu kamfanunuwan samar da wuta, irinsu Vital Vio, na tallan abin da suka kira wutar kashe kwayar cuta, amma wadannan za a iya sanya sune kawai a otel-otel ko manyan ofisoshi, saboda mafi yawan masu kasuwanci ba za su iya siyan irin wadannan fasahohi, a ganin Misis Clarke.
Gwada zafin jiki
Kamfanin fasaha na Flir ya na samar da kyamarar gwada zafin jiki da za a rika amfani da su a filayen jirgin sama da kuma jirgin 'yan sanda mai saukar ungulu shekaru da yawa, amma ya samu ci gaba a kasuwancinsa a 'yan watannin baya.
Yanzu kamfanin yana ta ganin jerin bukatu daga manyan masana'antu da wuraren kasuwanci.
"Gaskiya, kowanne kamfani na bukatar kare ma'aikatansa da abokan huldarsu," in ji mataimakin shugaban sashen kasuwanci na kamfanin Flir Ezra Merrill."
Kyamarar da ake sanya wa mutane mili mita biyar kusa da kumatu, wadda ake amfani da ita wajen auna zafin jikin dan adam, ba ta iya daukar bayanan masu sanya tabarau har sai sun cire shi.
Aikin ta ne ba da bayanai daban daban, kamar bayanan zafin rana ko kuma karfin ruwan sama, haka ma zafin jikin mutane.
Ana ta yin gwajin wannan fasahar a masana'antu daban-daban a Amurka, inda ake samun mabanbantan ra'ayi daga ma'aikata.
Kyamarar ba ta daukar hoto kwata-kwata kuma ba ta iya gane fuskar mutum ajikin hoto, amma Mista Merril ya yarda da cewa akwai nmaganar sirri, a kuma wasu wuraren zai iya zama hakan ya saba ka'ida.
"Wasu kasashen sun haramta bibiyar bayanan ma'aikata. Misali a Italiya akwai dokar da ta yi bayanin haramta bibiyar bayanin lafiya, kuma hakan ya hada da gwajin zafin jikin mutum.," in ji Clarke.
Mafi kyawun kofi
Wani Lauya Ravi Naik ya ce masu kamfanoni dole su yi taka tsan-tsan, ba kawai suna amfani da manhajar ba ne yadda ya dace.
"Wannan zai ba ka damar gane wanda zai iya aiki da wanda ba zai iya ba, in ba haka ba mene amfaninta? annan kamar wani kutse ne ga 'yancin dan adam".
Shugaban Bankin Barclays Jes Staley ya ce samun dubban ma'aikata a babban birni mai tsadar samun ofishi " zai iya zama wani abu da ya wuce" kuma aiki daga gida yayin wannan dokar hana fitar ya nuna mutane da yawa za su iya aiki daga gida yadda ya kamata.
A matsayinsa na wanda ya kirkiri real estate, Mista van Oostrom kwata-kwata bai yarda da wannan ba.
Yana ganin cewa, za mu kara ganin sabbin sauye-sauyen da zasu bai wa mutane damar aiki daga gida "za a zo lokacin da kamfanoni za su rika lallaba mutane su zo ofis".
"Mayar da ofis warin nishadi zai kara zama abu mai muhimmanci sama da ko yaushe" ya ce.