Coronavirus za ta iya kashe 'yan Afirka 190,000 a shekara ɗaya - WHO

Ana yi wa wani mutum gwajin cutar korona a Kenya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban WHO na Afirka ya ce killace masu cutar da ba su magani su ne mafita kawai
An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa cutar korona za ta iya kashe mutanen da suka kai 190,000 a nahiyar Afirka a shekarar farko da bullar ta idan matakan da aka dauka na yaki da ita suka gaza.

Hukumar, wacce ta bayyana haka a cikin wani bincike da ta gudanar, ta kara da cewa wannan adadi zai sa cibiyoyin kula da lafiya su yi cikar da ba za a iya shawo kan cutar ba.

Shugaban WHO a Afirka Matshidiso Moeti ya ce yaduwar cutar a nahiyar ba ta da yawa amma zai iya zama haifar da bullar cutar ta tsawon lokaci.

"Ko da yake mai yiwuwa cutar korona ba za ta yadu da yawa a Afirka kamar yadda take yi a wasu nahiyoyi ba, amma za ta iya jimawa a yankunan da ta yi katutu," in ji Dr Moeti.

Hukumar ta bayar da shawarar inganta fannin kiwon lafiyar nahiyar.

"Covid-19 za ta iya zama wani bangare na rayuwarmu nan da wasu shekaru masu zuwa har sai gwamnatoci sun dauki matakan gaggawa a nahiyar. Muna bukatar yin gwaji don gano masu dauke da cutar da gano su da kuma killace su, har ma da yi musu magani," a cewar Dr Moeti.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Wasu matakan da binciken ya yi nazari a kansu sun hada da matasan nahiyar ta Afirka wadanda "suka ci miroyar shirin kawar da cututtukun da ake yadawa irin su HIV da tarin shiƙa", da kuma raguwar mace-macen mata.

Me binciken ya gano?

Gargadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi ya zo ne daidai lokacin da kasashe kamar su Najeriya da Afirka ta Kudu da kuma Ivory Coast suka sassauta dokar kulle.

Binciken ya gano cewa tsakanin mutum miliyan 29 zuwa miliyan 44 za su iya kamuwa da cutar a yankunan da hukumar ke da ma'aikata a Afirka a shekarar farko ta bullar cutar korona.

Ta yi gargadin cewa mutum tsakanin 83,000 zuwa 190,000 za su iya mutuwa a cikin shekarar guda.

An yi binciken ne bisa hasashen kimiyya a kasashe 47 da ke da yawan mutane biliyan daga baki dayansu - amma kasashen Masar, Libya, Tunisia, Morocco, Eritrea, Sudan, Somalia da Djibouti ba sa cikin binciken.