Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump ya ce cutar coronavirus ta fi harin da aka kai Pearl Harbor muni
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cutar Korona a matsayin "hari mafi muni" da aka taba kai wa Amurka, yayin da ya kuma ci gaba da dora wa China laifin yaduwar cutar.
Mista Trump ya ce barkewar cutar ta mamaye Amurka fiye da harin bam din da Japan ta yi a tashar jirgin ruwa ta Pearl Harbor yayin Yaƙin Duniya na Biyu ko kuma harin 9 ga watan Satumbar 2011 shekaru 20 da suka gabata.
Gwamnatinsa tana kokarin daukan matakan ladabtarwa kan kasar ta China kan yadda take tunkarar cutar tun bullarta a birnin Wuhan.
Amma China ta ce Amurka na son karkatar da hankalin duniya game da yadda ta kasa tukarar annobar.
Tun lokacin da cutar ta bulla a birnin Wuhan na kasar China a watan Disamba, an tabbatar cewa cutar ta korona ta kama Amurkawa miliyan 1.2, bayan kashe kusan 73,000 da tayi.
Me ShugabaTrump ya ce?
Yayin da yake magana da manema labarai a ofishinsa da ke cikin Fadar Shugaban kasa, Mista Trump ya ce: "Mun fuskanci mummunan hari da aka taba kai wa kasarmu, wannan shi ne hari mafi muni da aka taba kaiwa.
"Wannan harin ya fi muni fiye da wanda aka kai kan tashar jiragen ruwanmu ta Pearl Harbor, wannan ya fi harin da aka kai cibiyar Ciniki ta Duniya. Ba a taɓa samun hari irin wannan ba."
"Kuma bai kamata hakan ta faru ba. Da an so da an dakatar da shi tun a tushe. China ta san alhaki na kan ta na dakile cutar. Ya kamata a dakatar da ita a tushe, amma ba ayi haka ba."