Matawalle ya nada sabon Sarkin Ƙauran Namoda

Asalin hoton, AB Kaura
Gwamnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Bello Mohammed (Matawallen Maradun), ya amince da nadin Alhaji Sanusi Mohammed a matsayin sabon Sarkin Ƙauran Namoda.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Zailani Bappa, ya aike wa manema labarai ranar Laraba ta ce gwamnan ya amince da nadin ne bayan shawarar da Majalisar Masarautar Ƙauran Namoda ta ba shi.
Alhaji Sanusi Mohammed ya maye gurbin Alhaji Mohamned Ahmed Asha wanda ya rasu ranar Lahadin da ta gabata.
Gabanin nadin nasa, sabon sarkin mai shekara 40 a duniya yana aiki a matsayin sojin Najeriya mai mukamin Manjo.
Sabon sarkin shi ne Sarki na uku a tarihin sarautar Sarki mai sanda ta Emir mai daraja ta ɗaya a Ƙauran Namoda, amma shi ne Sarki na 17 a masarautar Kiyawan Ƙauran Namoda.

Asalin hoton, AB Kaura







