Rikicin addini ya barke a sansanin 'yan gudun hijirar Nigeria na Kamaru

Asalin hoton, Getty Images
Wani rikici na addini ya barke tsakanin Musulmai da Kiristoci 'yan gudun hijirar Najeriya mazauna sansanin Minawao da ke cikin Kamaru a ranar Laraba.
Hakan ya kai ga an rusa gidaje da kona wasu na bangarorin biyu masu adawa da juna, musamman mazauna shiyya ta biyu da ta uku na sansanin.
Har wa yau, sun ji wa juna rauni da makamai. Sai dai jami'an tsaro sun shiga tsakani, abin da ya kawo lafawar rikicin.
Wakilin BBC a Kamaru, Mahamman Babalala ya ce alamu sun nuna cewa dukkan bangarorin 'yan asalin Jihar Borno ne da suka fito daga kananan hukumomin Goza da Bama.
Rikicin ya fara ne tsakanin yara biyu kanana (dan Kirista da dan Musulmi), inda suka kaure da dambe. Bayan mahaifin Musulmin ya raba su, sai mahaifin daya yaron ya ce ba a yi wa yaronsa adalci ba.
Iyayen biyu sun ci gaba da husuma tsakaninsu, kuma bayan labari ya shiga unguwanni sai rikicin ya zama na bambancin addini.







