An gano makarantar da ake tura mata da maza almajiranci

nASIR eL-rUFAI
An wallafa

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta rufe wata makaranta da ake tura kananan yara mata da maza karantun almajiranci, kuma ta kwashe dalibai sama da 300.

A wata zantawa ta wayar tarho da BBC, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya ce: "Abin ya tayar da mana da hankali, ya za a ce a gwama maza da mata almajirai a wuri daya?"

Ya ce shekarun kananan yaran da suka kwato daga makarantar da ke garin Zariya, ba su wuce takwas zuwa goma ba, amma dai suna ci gaba da bincike kafin fitar da cikakkun bayanai kan wannan al'amari.

Annobar koronabairas ta janyo zafafa matakan da hukumomi ke dauka a arewacin Najeriya kan karatun almajiranci, jihohi suke kwasar daruruwan almajran suna mayar da su hannun iyayensu.

A ranar Talata ne gwamnan jihar ya sanar da gano wasu almajirai guda biyar da jihar Kano ta mayar da su zuwa Kaduna, suna dauke da cutar korona.