'Mutum fiye da miliyan 50 ne ke gudun hijira a duniya’

An wallafa

Mutum miliyan 5.8 ne ke gudun hijira a fadin duniya saboda rikice-rikice ko kuma annoba, ga kuma cutar korona da ke kara zama barazana, kamar yadda rahoton ya yi gargadi.

Wani rahoton shekara-shekara da cibiyar da ke sanya ido kan harkokin 'yan gudun hijira (IDMC) ta fitar ya ce korona za ta iya kara jefa miliyoyin mutanen da tuni ke cikin matsi cikin karin hadari.

Sama mutum miliyan 45 ne aka tilasta musu barin muhallansu saboda rikici.

Wasu kari miliyan biyar kuma suka bar nasu saboda annoba kamar girgizar kasa da ambaliyar ruwa, in ji IDMC.

Ta kara da cewa adadin mutanen da ke gudun hijirar - saboda rikice-rikice da kuma annoba amma ba su bar kasarsu ba - yanzu ya yi sama sosai yadda bai taba yi ba.

Sabon adadin miliyan 33.4 na 2019 ya kara yawan adadin, wanda kuma shi ne adadi mafi girma da aka samu tun 2012.

Me ya sa ake tsere wa a bar gidaje yanzu sama da baya?

Sabuwar annobar korona ta jefa rayuwar da yawa daga cikin wadannan mutanen cikin bala'i na rashin tsafta wanda ke janyo musu samun muhalli na wucin gadi cikin gaggawa, da zama a wurare marasa tsari ba bisa ka'ida ba, da kuma janyo tururuwa cikin birane da ma karin wasu wahalhalun.

Wannan yawan da ake ruri daya kan janyo rashin ba da tazara da kuma tsafta wadanda duk matakai ne da aka bayyana na yaki da dakile yaduwar cutar korona.

Wannan annobar ta kuma takaita musu samun wasu kayan kare kai da kuma samun taimakon da ake bayarwa na agaji, kamar yadda daraktan IDMC Alexandra Bilak ya fada.

Ko da babu wannan annobar adadin 'yan gudun hijira a duniya abu ne mai tayar da hankali, kamar yadda sabon rahoton ya bayyana, cewa gazawar duka al'umma ce.

Cibiyar ta nemi gwamnatoci su hada hannu domin kawo karshen yakin basasar da ake yi a Syria, wanda ya tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu a watan Disamba domin kaucewa kuskuren da gwamnati ta yi a rikicin da aka fara shekara tara baya.

Ta kuma fito da girman rikicin da ke faruwa a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Yemen da kuma Afghanistan.

Rahoton ya ce akwai bukatar a dauki matakin gaggawa kan sauyin yanayi tare da shiri kan annoba, irin Guguwar Cyclones da ambaliyar ruwa da ta janyo wa miliyoyin mutane barin gidajensu bara.

Rahoton ya kuma yi kira da a bai wa wadannan 'yan gudun hijirar damar samun kulawar lafiya lokacin da ake tsaka da wannan annoba, kuma a ci gaba har zuwa wani lokacin don magance dalilan da ke janyo gudun hijira.

Cibiyar ta ce tana bibiyar yanayin kasar Iraki a nutse, inda nan ne aka fara samu rahoton mutum na farko dan gudun hijira da ya kamu da korona, da kuma kasashe irinsu Syria da Burkina Faso da kuma Colombia, wadanda tuni suke fama da wannan matsala ta 'yan gudun hijira kuma ake kara samun rahoton masu kamuwa da cutar.

Rahoton ya kuma bayyana wasu matsaloli da ke da alaka da wannan cuta. A Indiya, rahoton ya ce, a kalla ma'akatan ba da agaji 600,000 na fuskantar matsalar dokar hana zirga-zirga "Wanda ya tilasta musu komawa kauyukansu".

Yawancin 'yan gudun hijira ba su fiye yin tafiya mai nisa ba, ko dai don ba sa son yin nisa da ilayinsu ko kuma don ba su da kudin da za su tsallaka kasashen da ke makwabtaka da su.

Shi ya sa da yawansu ke makalewa a yankunan da kungiyoyin agaji ba sa kai wa, irin yankunan da ake yaki, suna ci gaba da dogara kan gwamantocinsu don kare su.

Wadannan gwamnatocin sau da yawa na zama dalilin da ke tilasta mutane gudun hijira, ko saboda yaki - ko kuma don gaza samarwa 'yan kasar wurin da za su zauna mai aminci.