Firai ministar New Zealand ta ce 'mun kawar da cutar Coronavirus

NZ PM Jacinda Ardern

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firai minista Jacinda Ardern ta kasar New Zealand
An wallafa

Kasar New Zealand ta sanar da cewa ta dakile yaduwar cutar korona tsakanin al'ummar kasar wanda ya kawo karshen cutar gaba daya.

A yanzu dai ba a samun masu kamuwa da cutar da suka wuce 9 a cikin kwanaki masu dama - inda daya kawai aka samu ranar Lahadi - matakin da ya sa Firai minista Jacinda Ardern ta ayyana cewa "a halin yanzu" sun kawar da cutar.

Amma jami'ai na kashedi ga 'yan kasar da ka da su yi sakaci, domin sun ce wannan nasarar ba ta na nufin babu wanda zai sake kamuwa da cutar ba ke nan.

Wannan labarin na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da gwamnati ta sassauta dokokin hana walwala mafi tsauri da kasar ta taba gindaya wa.

Daga Talata, wasu kamfanoni za su fara aiki, inda dukkan bangarorin kiwon lafiya da na ilimi za su koma bakin aiki.

Amma za a ci gaba da bukatar yawancin 'yna kasar da su ci gaba da zama a gida a koda yaushe.

A road sign in Wellington warning people to stay home and be kind

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Some non-essential business will be able to resume on Tuesday

"Mun fara bude sassa masu muhimmanci na farfado da tattalin arzikinmu, amma ba mu shirya kyale mutane su yi walwala ba tukuna", inji Ms Ardern yain ganawa da manema labarai da ta ke yi a kowace rana.

New Zealand na da kasa da mutum 1,500 da ke dauke da cutar korona inda cikinsu mutum 19 ne suka mutu.

A man is given an appointment slip by a security guard using a stick outside a COVID-19 coronavirus clinic

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda New Zealand ta rika gudanar da shirinta na dakile cutar korona: Tun wuri ta dauki mataki

Ms Ardern ta kuma ce "babu mutane masu yawa dauke da cutar a New Zealand", inda ta ce: "Mun yi nasara a wannan yakin".

Amma ta ce dole kasar ta ci gaba da daukan matakan kariya domin "muna son komai ya ci gaba da inganta".

Empty pubs and bars are seen on the Terrace, one of the most popular socialising locations in Christchurch

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun farkon bayyanar cutar korona kasar ta kulle dukkan wuraren da jama'a kan taru