Coronavirus: An yi kuskure a wajen jana'izar Abba Kyari – FCTA

Asalin hoton, Others
Hukumar Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja FCTA ta ce ta gano mutumin nan da aka gani a wani bidiyo a shafukan zumunta yana jefar da rigar kariya da ya sanya a lokacin da suka binne gawar Mallam Abba Kyari a Makabartar Gudu ranar Asabar.
A yammacin Asabar ne dai bidiyon ya karade shafiukan zumunta, musamman Twitter, dauke da wani mutum yana tubewa tare da jefar da kayan kariya na ma'aikatan lafiya da suka yi amfani da su wurin binne gawar.
Sai dai alamu sun nuna cewa ba iya abin da bidiyon ya nuna ba ne ya faru, an ga daidaikun safar hannu da aka zubar a kasa bayan hukumomi sun koma makabartar domin yin feshin magani da zummar kare yaduwar cutar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A wata sanarwa da FCTA ta fitar, ta ce sun gano dukkanin mutanen da ba su gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba a lokacin jana'izar.
Sannan hukumar ta ce yanzu haka an killace su, kuma za a yi musu gwajin cutar domin tabbatar da cewa ba su shafa wa wasu ba.
Kazalika ta sha alwashin cewa daga yanzu za a rika yin jana'izar duk wani mamaci bisa ka'idar hukumar NCDC.







