Abba Kyari: Rayuwar shugaban ma'aikatan Aso Rock Villa cikin hotuna

An wallafa

Mun zabo muku wasu daga cikin hotunan marigayi Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu bayan ya yi fama da cutar korona.

Malam Kyari mutum ne da ko daga nesa aka hango shi za a gane shi saboda yanayin shigarsa: yana yawaita sanya farin tufafi da jar dara.