Yadda matata ta haihu a dokar hana fita a Kano

Kano
An wallafa

Tun a daren ranar Alhamis ne mutanen Kano suka shiga cikin dokar hana fita ta tsawon mako guda domin yaki da cutar korona sai kuma ga matar Yakubu Abdu ta haihu.

Wasu bidiyo da hotuna da suka bulla a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an tsaro a Kano suke tabbatar da dokar hana fitar, inda suka rika saka wadanda suka yi kunnen kashi tsallen kwado.

Yakubu Abdu dan-gwangwan ne da ke yawo a fadin birnin domin zakulo karafa a cikin bola ko kuma shara.

"Matata ta haihu a jiya (Alhamis) kuma an garkame ni a cikin gida yau maimakon na fita neman abin da za ta ci ita da jaririn - ba tare da tsammanin tallafi daga wajen wani ba. Ina ganin wannan shi ne karshen tashin hankali," in ji Yakubu Abdu.

Kano
Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Tururuwar da 'yar kasuwa kan yi daga kasashen Nijar da Chadi zuwa Kano na taimaka wa tattalin arzikin jihar sosai, musamman a manyan kasuwar tufafi ta Kantin Kwari da kuma Kasuwar Dawanau ta hatsi.

Sani Moussa wani dan kasuwa ne da ke shiga garin Kano duk mako daga Maradi ta Nijar domin saro takalma da tufafi sannan ya karbo sautu daga wasu 'yan kasuwar.

Ya shaida wa wakilin BBC a Kano cewa: "Tabbas wannan dokar zaman gida za ta shafe mu sosai saboda a kan Kano muka dogara domin sayen kaya."

Wani babban malami a Kano ya fada wa BBC cewa: "Ba na goyon bayan dokar rufe masallatai saboda a ganina ba za ta taimaka wurin dakile cutar ba."

Talauci da addini ne kan gaba a yayin wannan doka a jihar da ke da mutum kusan miliyan 20, yayin da wasu ke cewa bin dokar tamkar mutuwa ce da yunwa.

Hukumomi a Kano sun ce sun tara tallafin fiye da naira miliyan 400 daga masu arziki a jihar domin tallafa wa marasa karfi bisa halin da matakan yaki da cutar korona za su saka su ciki.