Coronavirus: Afirka za ta zama cibiyar coronavirus in ji WHO

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa nahiyar Afirka ka iya zama cibiyar cutar korona nan gaba.

An samu karuwa sosai dangane da mutanen da ke kamuwa da cutar a nahiyar a makon jiya.

Mutum kusan 1,000 ne suka mutu sannan kimanin mutum 18,000 suka harbu da cutar ta korona a Afirka ya zuwa yanzu, ko da yake wannan adadi bai kai na Turai da Amurka ba.

Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniyar ta ce cutar na bazuwa daga manyan birane zuwa wasu yankuna a nahiyar.

Ta kara da cewa Afirka ba ta da isassun na'urorin da ke taimaka wa masu dauke da cutar korona yin numfashi.

Ya ya girman matsalar take a Afirka?

Akwai kusan mutum 19,000 da aka tabbatar na dauke da cutar korona a Afirka sannan akalla mutu 970 sun mutu a nahiyar mai yawan jama'a kimanin bilyan 1.3.

Kasashen Arewacin Afirka ne ke fama da cutar fiye da sauran sassan: Algeria da Egypt da kuma Morocco kowacce daga cikinsu na da fiye da masu dauke da cutar fiye da 2,000 inda akalla mutum 100 suka mutu a kowacce kasa.

Sai kuma kasar Afirka ta Kudu wadda ke da masu cutar fiye da 2,000 inda mutum 48 suka mutu. Ita kuwa Najeriya wadda ta fi kowacce kasa yawan jama'a a Afirka na da mutum 442 sannan mutum 48 sun mutu.

Me ya sa cutar ba ta yi yawa a Afirka kamar Turai ba?

Darektan Hukumar Lafiya ta Duniya mai kula da nahiyar Afirka, Dr Matshidido Moeti ta shaida wa BBC cewa tana kyautata zaton cewa batun tafiye-tafiye daga wata kasa zuwa wata ya taka rawa.

"Idan ku ka kalli yawan mutanen da suka yi bulaguro, Afirka na da karancin mutanen da suka yi tafiye-tafiye."

Amma tun da yanzu kwayar cutar tana kutsa Afirka ta ce hukumarta na tsammanin cutar za ta yadu kamar wutar daji.

Yanzu haka dai a cewar Dr Matshido Moeti cutar yana yaduwa a manyan birane kasashe irin su Afirka ta Kudu da Najeriya da Ivory Coast da Kamaru da Ghana.

Sai dai har yanzu akwai kasashen nahiyar ta Afirka guda 15 da cutar ba ta bazu da yawa ba kuma abin da hakan ke nufi shi ne idan kasashen suka ci gaba da daukar matakin bayar ta tazara to za su iya shawo kan cutar, in ji Dr Matshido.