Coronavirus: Har yanzu ban warke ba - El-Rufai

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce har yanzu bai samu sauki daga cutar korona ba.

El-Rufai ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Laraba.

"Har yanzu ban warke daga cutar covid-19 ba kuma da kaina zan bayyana hakan idan na warke. Ku guji yada labaran karya ko da kuwa kuna son yi," in ji gwamnan.

A ranar Laraba ne, gwamnatin jihar ta ce ta sallami mutum daya cikin mutane shida da suka kamu da cutar korona a jihar.

Gwamna El-Rufai ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona ne ranar 28 ga watan Maris.

Sai dai gwamnan ya ce har lokacin bai fara nuna alamun cutar ba amma ya killace kansa.

Sauran su ne:

Abba Kyari - Shugaban Ma'aikata a fadar gwamnatin Najeriya

Bala Muhammad - Gwamnan Bauchi

Seyi Makinde - Gwamnan Oyo

Muhammad Babandede - Shugaban hukumar kula da shige da fice

Sai dai tuni Bala Muhammad, Seyi Makinde da Muhammad Babandede suka bayyana cewa sun warke daga cutar korona.