Coronavirus a Nigeria: Jihohin da babu cutar coronavirus a kasar

An wallafa

Sannu a hankali cutar coronavirus na ci gaba da yaduwa a jihohin Najeriya bayan fara bullarta a Legas kudancin kasar.

Annobar ta fara bulla ne ranar 27 ga watan Fabrairun 2020, kuma zuwa ranar Talata 13 ga watan Afrilu, jihohi 19 ne da kuma Abuja aka tabbatar da bullar cutar coronavirus a Najeriya mai yawan jihohi 36 hadi da Abuja babban birnin Tarayya.

Alkaluma na baya-bayan nan daga hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce mutum 343 suka kamu da cutar a jihohi 19 na kasar hadi da Abuja. An sallami 91 daga cikinsu.

Zuwa ranar Talata 13 ga watan Afrilu cutar Covid 19 kashe mutum 10 a Najeriya.

Sai dai har yanzu akwai jihohi 16 na Najeriya da cutar ba ta shiga ba, wadanda suka hada da:

1. Abia

2. Adamawa

3. Bayelsa

4. Borno

5. Cross River

6. Ebonyi

7. Gombe

8. Imo

9. Jigawa

10. Kebbi

11. Kogi

12. Nassarawa

13. Plateau

14. Sokoto

15. Yobe

16. Zamfara

Jihar Legas da cutar ta fara bulla ta fi yawan wadanda suka kamu, inda zuwa ranar Talata ta ke da mutum 176. Sai Abuja babban birnin Tarayya inda 54 suka kamu.

Yawancin jihohin kudu maso yamma cutar ta fara bulla saboda makwabtakarsu da Legas.

Wasu na ganin yadda cutar ta fara shiga wasu jihohi a sassan yankunan Najeriya suna iya shafa wa makwabtansu.

Haka ma duk da gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta, amma idan ba a kara daukar matakai ba, kasashen da ke makwabta da Najeriya kamar Nijar da Kamaru da aka samu bullar cutar na iya shafa wa jihohin kasar da ke makwabta da su.

Sauran jihohin da cutar ta bulla a Najeriya sun hada da: Osun mai mutum 20 da Edo mai mutum 12 da Oyo mai mutum 11 da Ogun mai mutum 7 da Bauchi mai mutum 6 da Kaduna mai mutum 6 da Akwa Ibom mai mutum 5 da Katsina mai mutum 5 da Kwara mai mutum 4.

Sauran sun hada da Delta mai mutum 3 da Enugu mai mutum 2 da Ekiti mai mutum 2 da Rivers mai mutum 2 da Ondo mai mutum 2 da Benue mai mutum 1 da Niger mai mutum 1 da Anambra mai mutum 1 da kuma Kano mai mutum 3.

Tuni jihohin suka dauki matakai na hana fita da yin kira ga jama'a su dinga bayar da tazara tsakaninsu da wanke hannu domin dakile bazuwar cutar.