Hotunan Afirka na ranar 3-9 ga watan Afrilun 2020

An wallafa

Wasu zababbun hotuna daga Nahiyar Afrika.

Wasu yara na wasa a bakin ruwa a Mogadishu bababan birnin Somalia a ranar Juma'a 3 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu yara na wasa a bakin ruwa a Mogadishu babban birnin Somalia a ranar Juma'a duk da cewa 'yan sanda na kokarin korarsu a wani mataki na kare yaduwar coronavirus.
Mutane na bin layin karbar ruwa a Kibera, dake Nairobi babban birnin Kenya - Ranar laraba 8 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba, mazauna yankin Kobera slum a Nairobi babban birnin Kenya na kan dogon layin samun ruwan da gwamnati ke rabawa kyauta a taimako da take saboda coronavirus.
A dai ranar, wani yaro na tuka keke ta gaban wani zanen wata mata da yaro da takunkumi a fuskarta a yankin Mathare mai cinkoson jama'a a Nairobi, Kenya - Ranar Laraba 8 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A dai ranar, wani yaro na tuka keke ta gaban wani zanen Covid-19 a Nairobi
Presentational white space
Ma'aikata na hada takunkumi a ma'aikatar KICOTEC a Kitui dake Kenya - ranar Talat 7 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu ma'aikata na saka a wani kamfanin hada kayan sawa da ke garin Kitui a Kenya ranar Talata. Sun fara hana abobuwan kariya cikin sa'a 24 a kullum a wani matakin tunkarar Covid-19
Wani zane a bango dake nuna rabin fuska dauke da takunkumi da kuma kokon kai da babu takunkumin, a Khartoum dake Sudan ranar Laraba 8 ga watan Afrilu 2020.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani zane da ke nuna wa mutane sanya takunkumin fuska domin kare kansu daga cutar coronavirusa a wani bango a Khartoum, babban birnin Sudan ranar Laraba.
Likitocin kasar China sanye da takunkumi a Abuja Najeriya - ranar Laraba 8 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai ranar ta Laraba, likitoci kasar Chgina da suka sauka a filin jirgin saman a Abuja babban birnin Najeriya, domin taimakawa kasahsen yammacin Afrika wajen yaki da coronaviru.
Mai sai da kayan marmari a dauke da abarba a Abuja Najeriya - Ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A dai birnin a ranar Alhamis, wani mai tallan abarba yana neman masu saya a kan titi.
Wani dan kasuwa yana barci kusa da kankanar da yake sayerwa a Kampala dake Uganda. ranar Laraba 8 ga watan Afrilu 2020.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani dan kasuwa yana barci kusa da kankanar da yake sayerwa ranar Laraba a Kampala babban birnin Uganda. A wani bangare na takaita zirga-zirgar kasar masu sai da kaya dole suyi barci a kasuwa.
A dai ranar wata mage na leke daga kan taga a birnin Casablanca dake Moroco. Ranar Laraba 8 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai ranar wata mage na leke daga kan taga a birnin Casablanca dake Moroco.
Wani kare a Cape Town babban birnin Afrika ta Kudu yana leken ma'aikatan lafiya ranar Talata7 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani kare a Cape Town babban birnin Afrika ta Kudu yana leken ma'aikatan lafiya ranar Talata
Wani mutum sanye da takunkumi yana leka ma'aikatan lafiya a Bo-Kaap a Cape Town- ranar Latala 7 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Suna shiga gida gida a gundumar Bo-Kaap a wani mataki na tantance masu Covid-19 a fadin kasar
Ma'aikaciyar lafiya na koyawa yara yadda za su rika wanke hannu a Umlazi dake South Africa - Asabar 4 Afrilu 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A wani mataki na gangami a ranar Asabar, ma'aikatan lafiya na koyawa yara yadda za su rika wanke hannu a wani gari kusa da Durban.
Likitoci na taimakawa juna wajen sanya kayan kariya a Tunis dake Tunisia ranar Talata 7 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Likitoci na shirin duba wani mai fama da Covid-19 a Tunis babban birnin Tunusia, suna taimakawa juna wajen sanya kayan kariya ranar Talata.
Wasu babbin ma'aurata a titin Sidi Bou Said ranar Asabar 4 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu babbin ma'aurata a titin Sidi Bou Said ranar Asabar. Sun yi aure ba tare da halartar baki ba saboda Tunusia ta sanya kodar hana zirga zirga da taron jama'a
Wajen wani gyaran gashi a Bujumbura dake Burundi ranar Alhamis 9 ga watan Arfilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mata na yin kitso ranar Alhamis a wajen wani gyaran kai a Bujumbura bababn birnin Burundi, babu dokar hana fita saboda coronavirus.
Masu hada-hadar kudi ba bisa ka'ida ba a Harare a Zimbabwe - ranar Laraba 8 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu yan kasuwa dake abubuwansu ba bisa ka'ida ba a Harare babban birnin Zimbabwe suna amfani da damar sassauta dokar hana fita da aka bada a ranar Laraba.
Wani manomi da ya sanya takunkumi yana rufe shukarsa a Gaborone dake Botswana - ranar Lahadi 5 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani manomi da ya sanya takunkumi yana kare shukarsa daga tsintsaye a wajen Gabrone babban birnin kasar ta Botsuwana ranar Lahadi.
Mutane dauke da ganye a Dar es Salaam a Tanzania - ranar Lahadi 5 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mahalarta coci na addua tare da bada tazara kadan tsakaninsu yayin gudanar da ibada ranar Lahadi a Dar es Salaam dake Tanzaniya.
Mabiya darikar Orthodox na addu'a a birnin Addis Ababa dake Ethiopia - ranar Lahadi 5 ga watan Afrilu 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai ranar ta Lahadi, mabiya darikar Orthodox na gudanr da addu'a a wajen coci bayan yan sanda sun hana su shiga cikin cocin a Addis Ababa babban birnin Ethopia.

Images: AFP, EPA and Reuters