Coronavirus: 'Matsala ce ta siyasa, ba ta lafiya ba' - Yuval Noah Harari

An wallafa

"Zabin da muka yi na yaki da cutar Covid-19 zai sauya duniya nan da shekaru masu zuwa," in ji wani masanin tarihi dan kasar Isra'ila Yuval Noah Harari, marubucin littafin Sapiens: wanda ya yi magana kan takaitaccen tarihin dan Adam.

Wacce irin al'umma za mu zama lokacin wannan annoba? Ya kamata kasashe su zama tsintsiya madaurinki daya? Ko kuma kowa ya yi ta kansa? Tsare mutane da sanya ido kansu ne matakan da ya kamata a dauka kan 'yan kasa ko kuma kama-karya?

"Wannan rikicin ya sanya mu daukar tsauraran matakai kuma cikin gaggawa. Amma duk da haka muna da zabi," kamar yadda Harari ya shaida wa shirin BBC Newshour.

Rikicin "siyasa"

"Watakila zabi biyun da muke da su su ne, ko dai mu tunkari wannan matsala ta hanyar kowacce kasa ta ware kanta ko kuma hada gwiwa kan yakar abin da ya addabi duniya baki daya tare da nuna kishin juna,

"Na biyu a mataki na kowacce kasa, mu yi kokari mu ga bayanta ta hanyar tilasta wa 'yan kasa; komai ya koma hannun gwamnati ta kuma rika sanya idanu, ko kuma ta hanyar sadaukarwa tare da karfafa al'amuran 'yan kasa."

Annobar coronavirus ta janyo tambayoyi biyu, tambaya ta bangaren kimiyya da kuma siyasa, in ji Harari.

Amma yayin da muke warware kalubalen ta fuskar kimiyya, muna kuma daukar darasin yadda zamu tunkare ta ta fuskar siyasa.

"Duniya tana da duk abin da take bukata don cin galaba kan wannan annoba," kamar yadda yace.

"Yanzu ilimi ya wadata ba kamar lokacin annobar Black Death ba ne (wadda ta kashe kashi daya cikin uku da adadin mutanen nahiyar Turai) ba wai mutane na mutuwa bane ba tare da sanin dalili ba, ba kuma musan mai za mu yi a kai bane."

Tuni China ta bankado cewa cutar Sars-CoV-2 ita take haddasa wannan annoba, kuma kasashe da dama sun yi irin wannan bincike.

Kazalika Covid-19 bata da magani, masu bincike na ta fadi tashi wajen binciken rigakafin cutar ta hanyar fasahar zamani mafi inganci a fannin kiwon lafiya.

Mun kuma san rawar da matakan wanke hannu da ba da tazara ke takawa wajen kare mu daga cutar da kuma yadda suke hana yaduwarta.

"Muna sane da hadarin da ke fuskantarmu muna kuma da fasahar zamani, muna da karfin tattalin arziki da za mu iya cin nasara a kanta," in ji Harari.

"Tambayar kawai shi ne ta ya ya za mu yi amfani da wannan damar ta mu? wannan kuma tambaya ce da ke da alaka da siyasa."

Hadarin fasahar zamani

A wani mataki na ujula, ana watsi da abubuwan da tarihin ya kafa, matakan da ya kamata a dauka cikin shekaru sai a dauke su cikin dare daya. wannan ne gargadin da Harari ya yi a wani rubutu da ya yi a jaridar the Financial Times.

Fasahohin zamani da ke sanya idanu da aka kirkira masu cike da hadari, ana fara amfani da su ba tare da cikakkiyar fahimta akansu ba, ko kuma a kawo mutane su tattauna game da fara amfani da su.

Ya ce ana tafiyar da al'amuaran duniya ta yadda bai dace ba, gwanatoci na amfani da fasahohin kan bayanan mutane domin bin kwakkwafi da kuma yanke hukunci kan daidaiku a boye.

Kamar a Isra'ila, Gwamnati sun kara iko kan ayyukan sirri- ba kawai hukumomin lafiya ba - da ke sanin wuraren zaman daidai kun mutane. A koriya ta Kudu aka fara irin wannan sai dai a can a ana yi ne a bode domin 'yan kasa.

A China, in da nan ne aka fi samun amfani da wadannan fasahohin sa ido a duniya, an ta hukunta 'yan kasar da ke karya dokan hana fita da aka sa.

Cikin kankanin lokaci za ka iya bada hujjar wannan, kamar yadda Harari ya ce, Amma idon wadannan ci gaban fasahohin suka zama ma'aunin bibiyar al'amura anan gaba to akwai matsala.

"Ni ina bayan gwamnatoci kan tsauraran matakan da suka dauka a bangaren lafiya da tattalin arziki. Amma tun farko kamata yayi gwamnati dake wakiltar mutane ta yi."

"A lokacin da komi ke tafiya daidai, za ka iya jagorantar gwamnati da goyon bayan kashi 51 cikin dari na mutane. Amma a irin wannan lokaci, kana bukatar hadin kan duka mutane."

Kebe kai ko hadin kai

A shekarun baya bayan nan, Gwamnati na mulki ta hanyar raba mutane kashi biyu, yadda ake kirkirar kiyayya kan 'yan kasashen waje da kasashen su. In ji Harari.

Amma wannan matsalar lafiyar da ta addabi duniya ta nuna bata banbanta tsakanin kasashe da kuma kungiyoyin.

Ya kara da cewa, dole mu zabi hanyar da za mu bi, ko dai rarrabuwar kai ko kuma hadin kai mu manta da banbancin dake tsakaninmu.

Da yawan kasashe na kokarin yadda za su magance matsalar da kansu, ta yadda suke bukatar magunguna daga kamfanoni masu zaman kansu. An ta sukar Amurka saboda yunkurin tade wasu kasashen daga samun takunkumin fuska, da magunguna da kuma na'urar taimakawa nunfashi ta (Ventilators).

Akwai fargabar cewa allurorin da aka samar a dakunan gwajin kasashen da suka ci gaba ba za a bai wa kasashe masu tasowa da masu fama da talauci ba yadda suke bukata.

A yanzu, akwai yiwuwar a hada kai yau, kuma darasin da aka koya daga masana kimiyyar kasar China a jiya zai iya ceton rayukan mutane a Teheran a gobe, Kamar yadda Harari ya nuna.

Ya fi tafiya da tunani mai kyau, a samu hadin kan duniya baki daya, ta hanyar karfafa musayar ilimi da kuma ci gaba da ganin an magance tsoron dake damin duniya da kuma kasashen da wannan cuta ta sha.

"Za ka iya komawa tarihi baya lokacin da ilimi bai wadata ba kagani yaushe ne mutane suka kare kansu daga annoba ta hanyar kebe kawunansu,"

“Even in the Middle Ages, epidemics spread like the Black Death in the 14th century. So, going back to a medieval system won't protect us.”

Ko a karnikan baya an samu barkewar annoba kamar su Black Death a karni na 14.

Za ta iya sauya tsarin da aka halicce mu akai?

Ko wanne irin sakamako zabin da mukai ya haifar, Harari yayi Amannar za mu ci gaba a matsayinmu na " 'Yan Adan" kuma babu abin da zai sauya.

"Wannan cuta ta bayyana wani bangare mai kyau na halittar dan adan, shi ne jin kai da kuma kusantar wadanda ke fama da rashin lafiya.

Haka zalika ta bankado halin dan adam, maimakon ka shafa mana cutar, gwara mu samar da tazara tsakaninmu, mu nuna muna da wayo, kuma har cikin zuciyarmu haka abin yake.

Amma abune mawuyaci gare mu. Ina lokacin da wannan matsala ta zo karshe mutane za su sake jin suna bukatar yan uwansu ta hanyar jin balaransu lokacin cutar. Ina ganin ba za ta sauya komi ba game da rayuwarmu.