Coronavirus: Mutum 10 sun mutu a Nijar

An wallafa

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar mutum 10 da cutar coronavirus ta kashe tun bayan bullar cutar kasar.

Ana sa ran a yau Litinin ne Shugaban Nijer din, Mahamadou Issoufou zai yi wa 'yan kasar jawabi a karo na uku kan halin da jamhuriyar ke ciki dangane da annobar coronavirus.

Alkaluma na kara yin sama na wadanda ke kamuwa da ma mutuwa sakamakon annobar coronavirus a jamhuriyar.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar dai sun tabbatar da mutuwar mutum 10 da cutar coronavirus ta kashe tun bayan bullarta kasar.

Dakta Idi Illiassou Mainassara, ministan lafiya na Jamhuriyar Nijar ya ce mutum 13 suka warke a cikin 184 da suka kamu da wannan annoba zuwa yanzu.

Alkaluman da jami'ai suka fitar a jiya Lahadi na cewa mutum 40 sun sake kamuwa da cutar ta coronavirus.

Ministan lafiyar ya ce mutanen da suka rasu akasarinsu wadanda dama ba su da lafiya ne da ke fama da matsalar zuciya da huhu da ciwon suga.

"Lokacin da suka kamu ba su zo wurin likita ba da wuri, sai daga baya," inji shi.

Dama dai hukumar koli ta addinin Musulunci a Jamhuriyar Nijar ta sanar da soke tarukan sallar juma'a da sauran sallolin jam'i bayan hukumomi sun bayyana samun mutum na farko da cutar coronavirus ta kama a kasar.

Haka zalika, su ma jagororin addinin kirista sun bukaci mabiyansu su dakatar da tarukan ibada a coci-coci musamman ma dai na karshen mako.

Wadannan matakai sun faru ne kwanaki kalilan bayan hukumomin kasar sun sanar da rufe iyakokinsu don hana bazuwar annobar.