Coronavirus: 'Yan Najeriya da suka rasu a kasashen waje
Kawo yanzu alkaluma sun nuna akalla Najeriya ta rasa mutanenta guda hudu a Amurka da Birtaniya sakamakon cutar coronavirus da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.
Mutanen dai su ne:
- Alfaa Saadu
- Hajiya Laila Abubabakr Ali
- Dr Caleb Anya
- Bassey Effiong
Alfaa Saadu

Asalin hoton, Facebook
Alfa Sa'adu mai shekara 68 dai kwararren likita ne a Birtaniya inda ya yi aiki a asibitin Princess Alexandra na Cibiyar Insorar Lafiya ta Birtaniya, NHS Trust.
Sa'adu, wanda yake da sarautar Galadiman Pategi, dan asalin jihar Kwara ne da ke arewa maso tsakiyar Najeriya.
Galadiman Pategi ya kwashe shekaru kimanin 40 yana aiki a Birtaniyar kafin ya yi ritaya ya koma aikin wucin gadi.
Hajiya Laila Abubabakr Ali
Hajiya Laila Abubakar Ali 'yar Najeriya ce kuma 'yar asalin jihar Kano a arewacin kasar.
Laila mai shekara 60 ita ce 'yar Najeriya ta farko da ta fara rasuwa sakamakon annobar coronavirus a Amurka.
Marigayiyar ta rasu ranar 25 ga watan Maris a lokacin da take karbar magani a asibitin Lincoln Hospital da ke New York.


Dr Caleb Anya

Asalin hoton, Facebook
Dr Caleb likita ne a dan asalin karamar hukumar Ohafia da ke jihar Abia a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Marigayin ya rasu a kan aikinsa na taimaka wa marasa da ke fama da annobar coronavirus.
Dr Caleb ya rasu ranar 1 ga watan Afrilu.
Bassey Effiong

Asalin hoton, Facebook
Bassey Effiong mai shekara 25 shi ne matashin dan Najeriya kuma dalibi da ya rasu sakamakon annobar coronavirus.
Bassey wanda dalibi ne da ke shekarar karshe a tsangayar koyon aikin injiniya a jami'ar Western Michigan, Detroit da ke Amurka, ya rasu kwanaki kadan kafin kammala jami'ar.
Dalibin ya rasu ne ranar Asabar 28 ga watan Maris a asibitin Beaumont Hospital da ke Royal Oak.

A dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da nuna alhinin 'yan kasar tasu da suka rasu sakamakon annobar coronavirus, adadin mutanen da suka kamu da cutar a cikin kasar ya kai 232, kamar yadda hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta bayyana.
Kazalika NCDC ta ce 33 daga ciki sun warke daga cutar kuma an sallame su, inda biyar suka mutu.











