Liverpool da PSG na zawarcin Diomande,AIK Stockholm na son Yohanna

Yan Diomande

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yan Diomande
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool ta kara kaimi a zawarcin da ta ke yi wa dan wasan Ivory Coast Yan Diomande ta hanyar tuntubar kungiyar RB Leipzig ta kasar Jamus, wacce ba ta son ta sayar da dan wasan mai shekara 19. (Athletic - subscription required), external

Ita ma Paris St-Germain ta nuna sha'awar daukar Diomande din , wanda ya ce ya fi son komawa kungiyar ta Faransa (Telefoot, via Mirror), external

Arsenal na fuskantar hamayya daga Paris St-Germain a yunkurin dauko dan wasan Faransa Eli Junior Kroupi, mai shekara 19, daga Bournemouth da dan wasan Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, daga Atletico Madrid.(Independent), external

Brentford ta yi wa dan wasan Cologne na kasar Jamus Said El Mala mai shekara 19 tayin yuro miliyan 50. (Bild - in German), external

Sai dai, El Mala ya fadawa Brentford cewa ba ya son ya koma taka leda kungiyar da ke wasan firimiya. (Sky Sports Germany), external

Dan wasan Chelsea Marc Cucurella,mai shekara 27, na nazarin barin Stamford Bridge, ya yin da Atletico Madrid ke shirin zawarcin dan wasan kasar Sfaniya . (Teamtalk, external)

Juventus na son akalla kudi yuro miliyan 30 akan dan wasan Italiya Andrea Cambiaso, mai shekara 26 wanda Chelsea da Barcelona ke harinsa. (Calciomercato - in Italian), external

Dan wasan kasar Serbia Dusan Vlahovic zai bar Juventus idan kwantagarinsa ya zo karshe a karshen wata Yuni bayan da dan wasan mai shekara 26 ya yanke shawarar kin rattaba hannu kan sabuwar yarjejenya da kungiyar ta Italiya. (Football Italia), external

Juventus ta sake nuna sha'awar dauko dan wasan Crystal Palace da Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, kuma su na son dan wasan Atletico Madrid da Norway Alexander Sorloth, mai shekara 30. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

AIK Stockholm suna tattaunawa da dan wasan Nijeriya Zadok Yohanna mai shekara 18 wanda Brighton da Chelsea da kuma Newcastle United ke zawarcinsa. (Northern Echo), external