Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka daga 27 ga Maris - 2 ga Afrilu

An wallafa

Wasu zababbun hotunan wasu abubuwa da suka faru a Afirka a makon da ya gabata.

Mahmoud Saad (L) plays saxophone and Mohamed Adel (R) violin on their balcony during curfew in Giza, Egypt - Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu makada suna kade-kadensu a baranda a ranar Laraba a birnin Giza na Masar lokacin da aka sa dokar hana fita don hana yaduwar coronavirus.
A philosophy teacher gives a philosophy class for final year high school students filmed by Burkina Info TV in Ouagadougou, Burkina Faso - Monday 30 March 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin, aka dauki bidiyon wani malamin falsafa a Burkina Faso yayin da yake koyar da daliban ajin da za su kammala karatu. Wani gidan talbijin ne ke yada abin da ke faruwa a ajujuwa a kowace rana a yayin da makarantu da jami'oi ke rufe saboda annobar coronavirus...
People reading a blackboard news board in Monrovia, Liberia - Monday 30 March 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A wannan ranar ce dai mutane ke ta karanta labaran abubuwan da ke faruwa a kan allo dangane da annobar a babban birnin kasar Laberiya wato Monrovia.
A man with a child o his back cycling in Epworth, Zimbabwe - Tuesday 31 March 202

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum dauke da dansa a kan keke suna tafiya a wajen babban birnin Zimbabwe, Harare a ranar Talatar da ta wuce. Ita ma kasar an sanya dokar hana shiga da fita saboda coronavirus.
A horse and cart on a road which is being disinfected by municipal workers in Dakar, Senegal -Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba, ma'aikata suna aikin tsaftace tituna ta hanyar fesa ruwan maganin da ke kashe kwayoyin cuta a birnin Dakar na Senegal, domin kariya daga yaduwar Covid-19.
A man wearing what looks like a metal-disc as a mask in Kampala, Uganda - Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wanan rana kuma a babban birnin Uganda, Kampala, aka dauki wani mutum a hoto, yana sanye da wani irin takunkumin rufe fuska da ba a saba gani ba...
A Red Cross volunteer measures the temperature of a man at Nakasero market in Kampala, Uganda - Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Uganda ma an rufe ta, amma an bar wasu kasuwannin kasar a bude. A nan wani dan sa kai ne na kungiyar agaji ta Red Cross a ranar Larabar da ta wuce yake auna zafin jikin wani mutum da ke shiga birnin Kampala.
A Red Cross volunteer marks a person's arm with a tick at Nakasero market in Kampala, Uganda - Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Baya an tantance su, sai kuma a yi wa mutanen alama da maka don nuna cewa an duba su.
A woman pouring liquid soap into a bottle in Abidjan, Ivory Coast - Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A kasuwar Abidjan kuwa da ke Ivory Coast wata mata ce take hada sabulun ruwa a ranar Larabar da ta gabata. Daya daga cikin hanyoyin kariya mafi muhimmanci daga cooronavirus shi ne yawan wanke hannu da ruwa da sabulu.
A fisher seller at a market in Lagos, Nigeria - Monday 30 March 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mai sayar da kifi na kiran masu saye a wata kasuwar kayan abinci da ke birnin Legas a Najeriya a ranar Litinin din makon jiya, sa'o'i kadan kafin a rufe birnin.
A bread seller at a market in Kinshasa, DR Congo - Saturday 28 March 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar kuwa, wata mai sayar da burodi ce take shirya su a wata kasuwa da ke birnin Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, inda mutane ke ta rububin sayen kayan abinci.
People at a barbershop in Nairobi, Kenya - Tuesday 31 March 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane na kan layi don jiran a yi musu aski gabanin sanya dokar hana shiga da fita a birnin Nairobi na Kenya a ranar Talatar da ta gabata.
People holding their ID cards outside a government building in Mnihla, Tunisia - Monday 30 March 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu 'yan kasar Tunisiya suna neman a ba su tallafin kudi domin taimaka musu a yayin da suke kulle a gidajensu, a gaban wani ginin gwamnati a garin Mnihla ranar Litinin din da ta gabata.
People look out of a window in Rabat, Morocco - Friday 27 March 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne wasu 'yan Moroko ke leke ta taga a birnin Rabat, yayin da jami'ai ke korar mutane gida don bin dokar hana shiga da fita da aka sanya.
A police officer firing rubber bullets in Alexandra, South Africa - Tuesday 31 March 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani jami'in tsaro a Afirka Ta Kudu ya harba harsashin roba don tabbatar da cewa mutane sun yi biyayya ga dokar hana shiga da fita a birnin Alexandra a Talatar da ta gabata...
Shoppers sitting on trolleys in Durban, South Africa -Wednesday 1 April 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A wannan ranar ce kuma masu sayayya a birnin Durban na Afirka Ta Kudun suka zazzauna a kan kurar cefanensu don bin layin sayayya a gaban wani katafaren shago...
A man lying down on a deserted beach in Accra, Ghana - Monday 31 March 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Ghana kuwa a ranar Litinin da ta wuce, wani mutum ke yin kailula a gaban gabar tekun da babu kowa a birnin Accra, duk dai bayan da aka hana zirga-zirga.

Hakkin mallakar hotuna: AFP da EPA da kuma Reuters