Yaya lamarin annobar coronavirus yake a arewacin Najeriya?

Abba Kyari

Asalin hoton, Facebook/Buhari Sallau

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Mutanen da suka kamu da cutar koronabairas na ci gaba da karuwa a yankin arewacin Najeriya, inda adadinsu zuwa yanzu ya haura hamsin.

Hukumomi sun tabbatar da shigowar cutar Najeriya a karon farko ne ranar 27 ga watan Fabrairu, bayan wani mutumin kasar Italiya ya sauka a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Lagos, kafin ya tafi zuwa jihar Ogun mai makwabtaka.

Annobar koronabairas wadda ta gama duniya, ga alama ta fara bulla ne cikin yankin arewa ta Abuja babban birnin kasar.

Zai yi wuya a ce ga ranar da aka fara samun bullarta a Abuja, don kuwa hukumar dakile cutuka masu yaduwa mai alhakin fitar da bayanai a kan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya ta fara bayar da bayanan ne a dunkule.

Sai a ranar 22 ga watan Maris, ta sanar da cewa akwai mutum uku da ke fama da cutar a Abuja, lokacin da ta ce adadin masu koronabairas a fadin kasar ya karu da mutum hudu, inda yawansu ya kai 26.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Sai dai a wani sakon bidiyo da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Tiwita, an jiyo dansa Mohammed Atiku yana bayani daga cibiyar da aka killace shi, inda yake cewa shi ne mutum na farko da ya kamu da cutar a Abuja.

Ya ce an tabbatar da cutar a jikinsa ne ranar 20 ga watan Maris, bayan gwajin da aka yi masa.

An yi ta ka-ce-na-ce bayan mahaifin Mohammed ya sanar cewa dansa ya kamu da cutar covid-19, wasu sun rika yaba wa jarumtarsa ta fitowa ya yi wannan bayani ga jama'a, yayin da wasu suka rika zargin dan Atikun da rashin kebe kansa bayan ya dawo daga wata tafiya kasashen waje.

Daga bisani, a ranar Lahadin 22 ga Maris, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta sake fitar da sanarwa inda ta tabbatar da samun karin mutum na hudu da ya kamu da cutar sarkewar numfashin a Abuja

@NCDCgov

Asalin hoton, @NCDCgov

Bayanan hoto, Sau hudu hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC na fitar da sanarwa a kan mutanen da suka kamu da cutar koronabairas a wannan rana ta Lahadi

Washe gari ranar Litinin, yawan masu cutar koronabairas a Najeriya ya karu zuwa mutum 40, haka adadin masu cutar ma a birnin Abuja ya a ranar ya kai bakwai.

A wannan rana ce aka ba da sanarwar samun mutum na farko da ya rasu sakamakon wannan annoba a Najeriya, lamarin da ya faru a Abuja.

Hukumar NCDC ta ce mutumin dan shekara 67 ya dawo gida Najeriya ne bayan ya je ganin likita kasar Burtaniya, a cewarta mamacin ya yi fama da wadansu kwantattun cutuka kamar kansar cikin b'argo da kuma ciwon suga.

Achimugu

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Iyalin Engineer Sulaiman Achimugu sun wallafa wata sanarwa da ke cewa marigayin ya rasu ne ranar Lahadi, 22 ga Maris

Bayan kwana guda ne kuma, hukumar ta sake fitar da bayanin cewa an samu karin mutum biyu da cutar koronabairas ta harba a yankin arewacin Najeriya, inda a karon farko cutar ta bulla a wata jiha, baya ga babban birnin tarayya Abuja.

Ta ce mutanen biyu duk sun yi tafiya a baya-bayan nan zuwa kasashen Jamus da Burtaniya.

A ranar ta Talata ce, gwamnatin jihar Bauchi ta ba da sanarwar cewa, gwamnan jihar Bala Mohammed na daya daga cikin mutanen biyu da suka kamu da annobar koronabairas.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Kafin daga bisani, labarai suka fara zagayawa cewa koronabairas ta shiga fadar shugaban kasa. Hukumar NCDC dai ta ce ita dai ba ta karin bayanin a kan ko wane ne mutumin da ya kamu da cuta.

An ga fitattun mutane irinsu Atiku Abubakar na taya jaje ga shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin kasar, Abba Kyari, wanda gwamnati ta ki fitowa ta yi bayani kan rade-radin cewa ya kamu da cutar covid-19.

Daga bisani dai Malam Abba Kyari ya fitar da wata sanarwa wadda a ciki ya bayyana cewa zai koma Lagos don ci gaba da jinya a can.

Abba Kyari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abba Kyari

Ranar 25 ga watan Maris, adadin masu fama da annobar ya kai mutum 10 a Abuja, bayan sanar da karin mutum biyu da suka kamu.

Malam Nasir El-Rufa'i shi ne mutum na farko da aka bayyana cewa ya fara kamuwa da cutar koronabairas a jihar Kaduna ranar Asabar 28 ga Maris, yana cikin gwamnonin da suka fi zafafa daukar matakai don ganin annobar ba ta riski al'ummarsu ba.

Kafin nan adadin masu cutar ya karu a birnin Abuja daga mutum goma a ranar 25 ga wata zuwa mutum 14.

Kuma a karon farko cutar ta bulla a jihar Binuwai, inda hukumar NCDC ta ce zuwa ranar ta Asabar 28 ga watan Maris, adadin masu cutar a daukacin Najeriya ya kai 97.

A ciki an samu karin marasa lafiya biyu a Abuja da kuma guda a jihar Bauchi.

Da wayewar garin ranar Lahadi an ga karuwar masu fama da wannan annoba, zuwa mutum 21 a Abuja, bayan hukumar NCDC ta tabbatar da samun sabbin kamu biyar a ranar cikin babban birni.

Adadin ya kuma karuwa washe gari Litinin, inda a Abuja aka samu karin mutum hudu, haka zalika an tabbatar mutum biyu sun sake kamuwa a ranar cikin jihar Kaduna.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta sake tabbatar da samun mutum uku da koronabairas ta shafa a Abuja ranar Talata 31 ga watan Maris.

Bauchi

Asalin hoton, Twitter/@SenBalaMohammed

Bayanan hoto, Gwamnan Bauchi Sanata Bala Mohammed

Laraba 1 ga watan Afrilu a iya cewa tana cikin ranaku da aka samu adadin mutanen da aka tabbatar sun sake kamu mafi yawa a arewacin Najeriya, zuwa mutum 43.

Hukumar dakile cutuka ta ce an samu karin mutum bakwai da cutar ta shafa a Abuja, sai mutum 1 a jihar Kaduna da kuma karin wani a jihar Bauchi.

Bayan samun karin mutum biyar da suka kamu da cutar coronavirus a biranen Arewacin Najeriya, adadin masu fama da cutar a yanzu ya kai 54 cikin yanki.

Wadanne matakai hukumomi ke dauka?

Tuni dai, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin hana fita a daukacin babban birnin tarayya Abuja da ma wasu jihohi na kudancin Najeriya, Lagos da Ogun.

Ya ce manufar kulle biranen ita ce hana cutar ci gaba da bazuwa.

A sauran jihohi kuma irinsu Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa'i tun tuni ya kafa dokar ta-baci, inda ya umarci mutane su zauna a gida har a ga abin da hali zai yi.

Haka zalika, jihohi da dama a yankin sun ba da sanarwar rufe iyakokinsu, da nufin katse hanzarin kwayar cutar da hana shiga wuraren da zuwa yanzu ba ta riga ta je ba.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus