Mai gida ya yafe kudin hayar watanni saboda coronavirus

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Mutanen Afirka na yin wasu abubuwan ban mamaki kuma na tsere sa'a don taimaka wa wadansu a dai-dai lokacin da duniya ke fama da annobar koronabairus.

Nan ga wasu labarai masu faranta rayuka guda shida na wasu gwarazan 'yan Afirka.

1) Daga dinka tufafin kwalliya zuwa dinka rigunan likitoci

Masu dinka tufafin kwalliyar 'yan birni a kasar Libya sun koma dinka rigunan kariya na ma'aikatan lafiya.

Matan su shida suna dinka tufafin kariya ga likitoci da ma'aikatan jinya a wata masana'antar dinkin 'yan birni da ke Tripoli, babban birnin kasar Libya.

Dukkansu suna hakan ne a matsayin aikin sa-kai, wasu daga cikinsu ma a masana'antar suke kwana don sarrafa adadin tufafin kariyar likitocin da bukatarsu ta taso saboda annobar koronabairus.

Tuni sun dinka tufafin ma'akatan lafiya iri 50, har ma sun shiga kashi na biyu a aikinsu.

Ma'aikatan lafiya a wani asibitin birnin Tripoli sun yi maraba da kokarin matasan lokacin da suka tallata yunkurinsu a farkon wannan mako.

"Tunanin hakan ya zo ne lokacin da wani likita a asibitin al-Jalaa da ke Tripoli ya rika tuntubar masu sana'o'i daban-daban don su tallafa," Daya daga cikin masu gidan dinkin tufafin kwalliyar Najwa Taher Shokriy, mai shekara 26, ta fada wa wakiliyar BBC Rana Jawad.

Shekara guda ke nan da fara wannan sana'a tata ta dinki amma sai ta jingine burin fadadawa inda ta mayar da hankali wajen shawo kan matsalar annobar lafiya da ta taso.

Ita da tailolinta na son samar da karin tufafin kariya na ma'aikatan lafiya, ko da yake suna fuskantar tarnaki wajen samun kayan dinki a wannan birni mai fama da tashin hankali.

2) Masu sana'ar fure sun caba wa gidan kula da tsofaffi ado

Annobar koronabairas ta janyo dakatar da dumbin daure-dauren aure sakamakon haka an bar dumbin furannin da ake ado da su a irin wadannan bukukuwa suna bushewa.

Sai dai rukunin wasu masu harkar furanni a Paarl, wani gari a kasar Afirka ta Kudu sun hada kai inda suka ce da zaman banza gwamma aikin kishiya.

Da gudunmawar fure 600, sun caba ado ga fuskar wani gidan kula da tsofaffi na Huis Vergenoegd.

The residents were allowed out to see the display

Tun tsakiyar watan Maris aka killace mutanen da ke zaune a gida, ko da yake suna iya fita sararin farfajiya su sha kamshin furanni masu sanyaya rai.

Mutanen da kan wuce ta kusa da gidan kan tsaya su jinjina musu kan wannan kokari.

3) Hamshakin mai gidan haya ya yafe kudin gida

Wani mai gidan haya a Kenya ya fada wa 'yan hayansa su 34 cewa kada su biya kudin haya na watannin Maris da Afrilu saboda ya fahimci cewa annobar koronabairas ta sanya su cikin mawuyacin hali.

Michael Munene ya mallaki gida mai sashe 28 a Nyandarua da ke yammacin kasar, inda yake karbar shilling 3,000 kwatankwacin naira 11,000 a matsayin kudin hayar daki duk wata.

Yana kuma da sashen kasuwanci a rukunin gidajen inda ya ba da haya a kan shilling 5,000 kwatankwacin naira 17,000 duk wata. Idan duk 'yan hayarsa ba su biya shi kudin ba, to wannan mai gida zai rasa kudi kwatankwacin naira 750,000.

Mista Munene dai tuni ya samu yabo bayan ya fada wa wani gidan talbijin din Kenya cewa ya gwammace 'yan hayarsa su ciyar da 'ya'yansu a kan ya amshi kudin hayar..

Shi ma ya taba zama dan haya kuma har mai gidan da ya zauna ya taba rufe masa daki saboda bai iya biyansa kudi ba, in ji Michael Munene.

"Suna zaune a gidana tsawon wani lokaci kuma kudin da suke biyana ya taimaka mini sosai a rayuwata," a cewarsa.

4) Gwanar rawa da ciki na debe wa mutane kewa a intanet

Gwanar rawa da ciki 'yar kasar Tunisiya, Nermine Sfar tana fitar da bidiyon yadda take takawa da nufin debe kewa ga mutanen da ke zaune a gida saboda matakan kulle da aka sanya a kasar ta Arewacin Afirka.

Tana dai haska rawarta ne kai tsaye a kowanne dare ta Facebook daga gida kuma miliyoyin mutane ne suka kalli raye-rayen nata a Facebook tun daga makon jiya.

Ta sanya wa gangamin nata a shafukan sada zumunta: "Ku zauna a gida. Zan muku rawa".

Ga alama kuma kwalliya ta biya sabulu - don kuwa dubban daruruwan mutane ne a kullum suke kallon bidiyonta, har ma akwai wani bidiyo da ta yi a makon jiya wanda aka kalla sau kusan miliyan biyu

5. Mawakiya ta ba da gida a mai da shi cibiyar kebe masu covid-19

Wata tauraruwar mawakiya a kasar Habasha ta ba da gudunmawar wani gida don a yi amfani da shi ga mutanen da akan kebe bayan sun kamu da annobar koronabairas.

A cikin watan jiya ne, gwamnatin Habasha ta ba da umarni a kebe duk masu isa kasar a wani otel, wanda su ne za su biya kudin daki har tsawon kwana 14.

Hamelmal Abate, wadda ta samu daukaka a shekarun 1990 da wakokinta na harshen Amharic da Afaan Oromo ta fada wa wakilin BBC a kasar Habasha Kalkidan Yibeltal cewa gidan zai burge bakon da ya sauka ba shi da ko koko.

"Su ma mutanen da ake bukatar a kebe, ai namu ne," in ji mawakiyar.

"Wasu, wadanda ke dawowa daga ketare suna iya kama otel su zauna don wannan manufar. Amma akwai wadanda ba su da halin kama daki. Su ma suna bukatar a darjanta su."

Gidan da Hamelmal ta bayar aron yana kusa da inda take zaune a Addis Ababa, babban birnin kasar.

Tana cikin 'yan kasar Habasha da akan samu suna bayar da gudunmawar gidajensu don su zama cibiyoyin kebe mutane yayin da ake samun karin damuwa game da karancin wuraren da ake bukata don kebe mutane.

6) Gola ya saya wa magoya bayansa abinci

Wani gola da ke buga wasa a gasar firimiyar Najeriya ya bai wa magoya bayansa hudu kudin da za su tabbatar sun iya sayen abincin da za su ci a wannan lokaci da ake fama da annobar koronabairas.

Mai tsaron gidan kungiyar Plateau United Chinedu Anozie ya ba kowanne daga cikin magoya bayan nasa hudu kudi naira 5,000.

Ana iya cewa ai wannan ba wani kudin kirki ba ne, amma fa a fahimta, akasarin 'yan kwallo a gasar firimiyar Nijeriya mai yiwuwa suna daukar abin da bai fi 35,000 ba ne a duk mako, a cewar wakilin BBC Nduka Orjinmo da ke Legas.

Baya ga kokarin bayarwa, Jaridar Najeriya ta Vanguard ta nunar cewa gola Anozie gwani ne wajen tare kwallo shiga ragarsa.

Ba a iya samun nasara a kansu ba cikin wasa goma da suka buga - kuma kungiyarsa ce ke saman tebur a gasar, ko da yake yanzu an dakatar da ita saboda annobar duniya.