Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: Ana kara samun mutanen da ke warkewa a Najeriya
Yayin da a kullum ake kara samun yawan masu dauke da coronavirus a Najeriya, yawan wadanda kuma ke warkewa daga cutar na karuwa a kasar.
Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriya ta ce zuwa yanzu mutum 25 ne aka yi nasarar yi musu magani a cibiyoyin kula da masu cutar koronabairus.
Mutum 210 ke da cutar a Najeriya, kamar yadda alkalumman hukumar NCDC mai hana yaduwar cutuka a kasar suka nuna.
Gwamnatin Legas inda adadin masu fama da cutar ya fi yawa, ta ce mutum 23 sun warke daga cikin wadanda suka kamu da coronavirus.
A wani sakon da ya wallafa a Twitter, gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya jinjina wa kokarin da ma'aikatan lafiya ke yi, bayan tabbatar da yawan wadanda suka warke.
Tun da farko gwamnatin Legas ta sanar da karin wadanda suka warke kafin cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta wallafa nata alkaluma inda ta yi nuni da cewa an samu karin mutum biyu da suka warke daga cutar.
Ba ta dai fito ta rarrabe jihohin da aka samu mutanen da suka warke din ba, amma dai jihar Legas ce ke da kaso mafi yawa.
Mutum hudu zuwa yanzu sun mutu a Najeriya, tun bayan bullar cutar a ranar 27 ga Fabrairu a kasar.
Cutar ta kama manyan jami'an gwammnatin kasar da suka hada da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyari da shugabanan hukumar shige da fice ta kasa Muhammad Baban Dede da kuma gwamnonin jihohin Bauchi da Kaduna da Oyo.
Sama da mutum miliyan daya yanzu ke dauke da annobar coronavirus a duniya
Sama da mutum 51,000 cutar ta kashe a duniya, yayin da sama da mutum 208,000 suka warke, a cewar alkaluman jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka.
Amurka ce ta fi yawan masu dauke da cutar, yayin da cutar ta fi yin kisa a Italiya.
Cutar ta fara bulla ne a China watanni uku da suka gabata.
Karin labaran da za ku so ku karanta