Covid-19: Yadda aka gina asibitin coronavirus cikin kwana 9 a London

Asalin hoton, Getty Images
Sabon asibitin Birtaniya ma fi girma da aka gina cikin kwana tara domin majinyatan coronavirus ya fara aiki.
An mayar da ExCeL exhibition centre, katafaren wurin da ake taruka da bukukuwa ne a gabashin London, zuwa asibitin coronavirus.
Asibitin na da girman da ke kunshe da gadajen majinyata 4,000.
Cikin kwana tara aka sauya katafaren babban dakin taron mai girman kafa 87,328 zuwa asibiti da ke da bangarori sama da 80, kowanne dauke da gado 42. Akwai kuma gadaje kusan 500 na zamani da ke dauke da na'urorin taimaka wa majinyaci shakar iska da ake kira ventilators.
Akwai kuma wani bangare da ke da wasu gadajen 3,500.
Idan har aka kammala, zai kasance daya daga cikin manyan asibitoci a duniya.


Ta ya aka gina ta?
Asibitin, wanda aka bude a ranar Juma'a, an gina shi ne tare da taimakon sojoji sama da 200 a rana tare da jami'an ma'aikatar lafiya da kuma 'yan kwangila.

Asalin hoton, Getty Images
Injiniyoyi daga BDP, kamfanin da ya taimaka wajen sauya babban dakin taron zuwa asibiti, suna cikin wadanda suka samar da cibiyar domin ceto rayuka.
Jagoran BDP James Hepburn ya ce lokacin da aka dauka wajen ginawa ba kamar aikin gina sauran cibiyoyin lafiya ba inda sai injiniyoyi sun gabatar da tsarin ginin.
Ya ce an yi amfani da kayayyakin da ke dakin taron wajen samar da gadaje.
Za a ci gaba da gina irin wannan asibitin a wasu biranen Birtaniya domin yaki da coronavirus a kasar inda cutar ta kashe sama da mutum 2,000.
A wasu wuraren kuma za a mayar da filayen wasanni zuwa wuraren kula da masu cutar coronavirus












