Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Yar Buhari ta kammala killace kai lafiya
Uwar gidan Shugaba Buhari Aisha ta sanar da cewa 'yarta kamala killace kanta na mako biyu da ta yi bayan komawarta Najeriya daga Birtaniya inda coronavirus ta fara yaduwa a can.
Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram cewa "abun farin ciki ne na sake yin ido biyu da diyata bayan kwashe mako biyu a killace. Ina yi wa duk masu cutar fatan waraka sannan ina fatan Allah zai kawo karshen wannan annoba."
Kimanin mako biyu kenan dai Aisha Buhari a wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce a ranar Alhamis ne 'yar tata wacce ba ta fadi sunanta ba ta koma Najeriyar daga Birtaniya.
Ta ce yarinyar ta killace kan nata ne saboda shawarar da Ministan Lafiya na kasar suka bayar ba wai don ta nuna alamun cutar ba.
Kuma ta yi kira ga iyaye su dauki iirn wannan matakin idan yaransu sun koma kasar daga tafiya.
Kazalika uwargidan shugaban kasar ta ce ta rufe ofishinta na tsawon mako biyu saboda wasu ma'aikatan ofishin nata sun dawo daga Birtaniya.
Aisha Buhari ta kuma yaba wa gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya bakwai da na jihar Neja da Kwara kan matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar.
Ta kara yin kira ga mutane da su ci gaba da bin shawarwarin jami'an lafiya don kauce wa yaduwar cutar.