Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An sa dokar hana fita a Makka da Madina
Kasar Saudiyya ta sanar da sanya dokar hana fita na awa 24 a birnin Makkah da Madina da za ta fara aiki yau Alhamis.
Wannan dokar dai kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta rawaito kamfanin dillancin labarai na kasar, har sai baba ta gani.
Dokar ta tanadi cewa mutane za su fita waje ne kawai bisa biyan bukatar neman abinci ko asibiti kuma za a yi hakan ne tsakanin karfe 6 na safe zuwa 3 na ranar kowace ranar.
Har wa yau, dokar ta hana shiga ko fita daga biranen amma ta kebance jami'an tsaro da ma'aikatan lafiya da 'yan jarida.
Wannan doka dai wani mataki ne da gwamnatin kasar Saudiyya ta dauka da manufar shawo kan annobar coronavirus a biranen guda biyu.
Ma'aikatar lafiyar kasar dai ta ce kawo yanzu kasar na da mutum 1,885 da ke dauke da cutar coronavirus, inda mutum 21 suka rasu sannan 328 suka warke.