Coronavirus: An hana cin mage da kare a Shenzhen na China

A cat waiting to be adopted looks out of its cage at the Royal Society for the Prevention of Cruelty to Animals (RSPCA)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin 'yan China ba su fiye cin naman Kare ba da mage
An wallafa

Shenzhen ya kasance birni na farko a China da ya haramta sayarwa da cin naman kare da mage.

Wannan na zuwa ne bayan alakanta cutar coronavirus da cin namun daji, dalilin da sa ya hukumomin China suka haramta ci da sayar da naman dabbobin.

Dokar haramta cin mage da kare za ta fara aiki ranar 1 ga watan Mayu a Shenzhen.

Wata kungiyar kare hakkin dabbobi ta (HSI) ta ce karnuka miliyan 30 ne ake kashewa a sassan Asia domin nama.

Sai dai ba a fiye cin naman kare a China ba- yawancin 'yan China sun ce ba su taba ci ba kuma ba za su ci ba.

"Kare da mage sun fi shakuwa da mutane fiye da sauran dabbobi, kuma haramta cin naman kare da mage ba sabon abu bane a kasashen da suka ci gaba har da Hong Kong da Taiwan," kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuter ya ruwaito gwamnatin birnin Shenzhen na cewa.

Kungiyar HSI ta yaba wa Shenzhen da daukar matakin.

"Wannan yunkuri ne da zai kawo karshen mummunan kasuwancin da ke kisan kusan karnuna miliyan 10 da mage miliyan 4 a China duk shekara," in ji Dr Peter Li, jami'in HSI.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Kasuwar naman dabbobin daji

A watan Fabrairu ne hukumomin China suka haramta cin naman dabbobin dawa.

Matakin na zuwa ne bayan ta bayyana cewa kasuwar Wuhan da ake sayar da namun dajin nan ne tushen barkewar cutar coronavirus, inda ake tunanin daga dabbobin aka samu cutar.

Yadda ake ta yada labarai game da cin naman dabbobin ne ya sa gwamnatin China ta fara daukar matakai kan kasuwannin da ake sayar da naman dabbobin dajin.

Kasuwar nama a Shenzhen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata kasuwar nama a China

Kusan mutum miliyan daya yanzu ke dauke da coronavirus a duniya, inda sama da mutum 47,000 suka mutu, kamar yadda alkalumman Jami'an Johns Hopkins suka nuna.

A China kawai, mutum 81,589 ke dauke da cutar kuma mutum 3,318 suka mutu, in ji hukumar lafiya ta kasar.

Masana kimiya da masu bincike har yanzu ba su samo maganin cutar ba da kuma abin da ya haddasata da kuma yadda ta yadu ga bil adama.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne