Turkmenistan ta haramta kalmar 'coronavirus'

An wallafa

Turkmenistan ba kasar da ake jin labarinta ba ce a-kai-a-kai - an fi saninta da gwamnatin kama-karya da kuma arzikin iskar gas mai dumbin yawa.

Sai dai kasar, wadda ke tsakiyar nahiyar Asiya, ta tsaurara mataki game da amfani da kalmar 'coronavirus'; hasali ma an haramta amfani da ita kwata-kwata a kasar.

Tuni kafar yada labaran kasar ta daina amfani da kalmar sannan aka cire ta daga takardun bayanan lafiya, a cewar rahoton kungiyar 'yan jarida ta Reporters Without Borders (RSF).

'Yan sanda a kasar za su iya kama mutanen da suka sanya takunkumin rufe fuska ko kuma suke yin hira a kan kalmar ta coronavirus.

Turkmenistan na daya daga cikin kasashen duniya da ba a sanin halin da take ciki.

Gwamnati tana da cikakken iko kan kafafen yada labarai na kasar sannan kuma ta rufe shafukan intanet na kafafen watsa labarai na kasashen waje (kamar na BBC) a kasar.

Zuwa yanzu kasar ba ta bayar da rahoton bullar cutar a kasar ba, amma makociyarta Iran tana da mutum sama da 47,000 da suka kamu.

Daga ranar Talata 31 ga watan Maris fiye da mutum 800,000 ke dauke da coronavirus, inda mutum fiye da 39,000 suka mutu sakamakon cutar a fadin duniya.

Karin labaran da za ku so ku karanta