Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Yadda Abuja da Lagos suka kasance a rufe
An wallafa
An wayi garin Talata da dokar hana zirga-zirga a garuruwan Legas da Abuja da kuma Ogun a Najeriya.
Dokar ta biyo bayan umarnin da shugaban kasar ya bayar a ranar Lahadi inda ya umarci rufe iyakokin jihohin da kuma takaita zirga-zirga a jihohin a yunkurin yaki da cutar coronavirus.
Za a shafe kwanaki 14 cikin wannan dokar kamar yadda shugaban ya bayyana, ga wasu daga cikin hotunan yadda aka wayi a birane ranar Talata a jihohin.