Coronavirus: Yadda Abuja da Lagos suka kasance a rufe

An wallafa

An wayi garin Talata da dokar hana zirga-zirga a garuruwan Legas da Abuja da kuma Ogun a Najeriya.

Dokar ta biyo bayan umarnin da shugaban kasar ya bayar a ranar Lahadi inda ya umarci rufe iyakokin jihohin da kuma takaita zirga-zirga a jihohin a yunkurin yaki da cutar coronavirus.

Za a shafe kwanaki 14 cikin wannan dokar kamar yadda shugaban ya bayyana, ga wasu daga cikin hotunan yadda aka wayi a birane ranar Talata a jihohin.

Legas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sanda kenan suka saka shingayen tare hanya kan iyakar da ke tsakanin jihohin Legas da Ogun a daidai Ojodu-Berger.
Wasu jami'an soja kenan ke tsayar da motoci a Unguwar Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Bayanan hoto, Wasu jami'an soja kenan ke tsayar da motoci a Unguwar Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Wasu mazauna unguwar Karu kenan da ke Abuja yayin da wasu mazauna unguwar ke kokarin fita duk da dokar da aka sa.
Bayanan hoto, Wasu mazauna unguwar Karu kenan da ke Abuja yayin da wasu mazauna unguwar ke kokarin fita duk da dokar da aka sa.
Yadda kasuwar Wuse a Abuja ta zama kamar kufai, ga kuma baro da dama an tara wuri daya alamar cewa babu hada-hadar masu yin dakon kaya.
Bayanan hoto, Yadda kasuwar Wuse a Abuja ta zama kamar kufai, ga kuma baro da dama an tara wuri daya alamar cewa babu hada-hadar masu yin dakon kaya.
Yadda babbar hanyar Ikorodu ta Legas ta zama wayam sakamakon dokar hana fita da aka saka a jihar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda babbar hanyar Ikorodu ta Legas ta zama wayam sakamakon dokar hana fita da aka saka a jihar.
Babbar hanyar Sani Abacha a Abuja kenan tamkar an yi shara a ranar Talata.
Bayanan hoto, Babbar hanyar Sani Abacha a Abuja kenan tamkar an yi shara a ranar Talata.
Daya daga cikin jami'an kiyaye hadura na jihar Ogun ke kokarin toshe hanyar da za ta shiga Legas a daidai iyakar da ke tsakanin jihar ta Ogun da Legas.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daya daga cikin jami'an kiyaye hadura na jihar Ogun ke kokarin toshe hanyar da za ta shiga Legas a daidai iyakar da ke tsakanin jihar ta Ogun da Legas.