Yadda Coronavirus ta yadu a Nigeria

Asalin hoton, Getty Images
Za a iya cewa tun watan Disamban 2019 al'ummar duniya ta shiga cikin wani irin yanayin rudu sakamakon bullar annobar coronavirus wadda ta fara a birnin Wuhan da ke kasar China.
Wannan annoba dai ta shafi mutum fiye da 730,000, inda fiye da mutum 34,000 suka mutu a fadin duniya.
A Najeriya, annobar ta fara bulla ne ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 a birnin Legas, inda kuma kawo yau din nan, mutum 131 ne suke dauke da cutar a fadin kasar.
Mutum biyu ne suka rasu sakamakon cutar, inda aka sallami mutum uku bayan sun warke.
Ga ranaku da jihohin da 'yan Najeriyar suka kamu da cutar ta coronavirus:
- 30 ga watan Maris 2020 - Mutum 21 - Legas (13), Abuja(4), Kaduna (2), Oyo (2).
- 29 ga watan Maris 2020 - Mutum 14 - Legas (9), Abuja (5)
- 28 ga watan Maris 2020 - Mutum 16 - Legas (7) , Abuja (2), Oyo (4), Kaduna (1) , Benue (1) da kuma Osun (1).
- 27 ga watan Maris 2020 - Mutum 16 - Legas (8), Abuja (3), Oyo (2), Enugu (2), Edo (1).
- 26 ga watan Maris 2020 - 14 - Legas (12), Abuja (1) da kuma Bauchi (1).
- 25 ga watan Maris 2020 - Mutum 7 - Abuja (2), Legas (3), Rivers(1) da Osun (1).
- 24 ga watan Maris 2020 - Mutum 4 - Legas (1), Ogun (1), Abuja (1) da Bauchi (1).
- 23 ga watan Maris 2020 - Mutum 9 - Abuja (3), Legas (5) da jihar Edo (1)
- 22 ga watan Maris 2020 - Mutum 8 - (6) a Legas, (1) a Abuja, (1) Oyo.
- 21 ga watan Maris 2020 - Mutum 10 - (7) a Legas da (3) a Abuja.
- 19 ga watan Maris 2020 - Mutum 4 - masu dauke da cutar sun koma kasar daga kasashen waje.
- 18 ga watan Maris 2020 - Mutum 5 sun koma kasar daga Burtaniya ko Amurka
- 16 ga watan Maris 2020 - Wata mace guda daya ta kamu da cutar coronavirus bayan kwanaki uku da komawarta Legas daga Burtaniya.
- 08 ga watan Maris 2020 - Mutum daya ya kamu da coronavirus a jihar Ogun
- 27 ga watan Fabrairu 2020 - Gwaji ya nuna wani mai shekara 44 dan kasar Italiya ya kamu da cutar ta coronavirus a Lagos.
Jihohin da masu dauke da cutar coronavirus suka fito:
- Lagos - 81
- Abuja - 25
- Ogun - 3
- Ekiti - 1
- Oyo - 8
- Edo - 2
- Bauchi - 2
- Osun - 2
- Rivers - 1
- Enugu - 2
- Benue - 1
- Kaduna - 3


A watan Disambar bara duniya ta san da coronavirus, amma yadda ta kankane duniya, sai a ga kamar ta dade da bayyana.
Cutar ta fito ne daga Wuhan a China a karshen shekarar 2019, inda aka gano wasu masu dauke da ita a wata kasuwar sayar da nama.
Coronavirus, wadda a hukumance ake kiranta Sars-CoV-2, na da alaka ta kusa-kusa da wasu cutuka da ke shafar jemagu, sai dai ana tunanin ita wannan cutar jemagun ne suka shafa wa wata dabba da ba a gano ko wacce iri ba ce, ita kuma ta shafa wa mutane.
Har yanzu dai ba a gano takamaimai asalin dabbar ba, don haka tana iya ci gaba da yada wa mutane cutar.












