Firai Ministan Burtaniya Boris Johnson ya kamu da coronavirus

Asalin hoton, Reuters
Firai Ministan Burtaniya Boris Johnson ya kamu da coronavirus, a cewar fadarsa ta Downing Street.
Mr Johnson ya nuna alamun cutar saisa-saisa kuma tuni ya killace kansa a fadar Downing Street.
Wata sanarwar da fadar ta fitar ta ce "Sakamakon gwajinsa ya nuna yana dauke da cutar, kuma ya yi gwajin ne bisa shawarar da babban likitan gwamnatin kasar Farfesa Chris Whitty ya ba shi.''
Sai dai zai ci gaba da jan ragamar gwamnatin na yaki da cutar kamar yadda sanarwar ta kara.
Ma'aikatan Hukumar Inshorar Lafiya Ta Ingila NHS ne suka yi masa gwajin a fadar tasa.
A wani sakon Twitter da ya wallafa, Boris Johnson ya ce: ''Cikin sa'a 24 da suka gabata ina ta jin alamun cutar sama-sama kuma an yi min gwaji ya tabbata ina dauke da coronavirus.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
''A yanzu haka na killace kaina, amma zan ci gaba da jan ragamar gwamnati yadda muke yaki da ita ta sakon bidiyo.
''Za mu yi aiki tare wajen shawo kan wannan annoba.''


Ranar Alhamis da daddare ne lokaci na karshe da aka ga firai ministan a waje, lokacin da yake tafa wa ma'aikatan NHS a kofar fadarsa don jinjina wa kokarinsu.
A yanzu haka an samu masu dauke da cutar 11,600 a Burtaniya, kuma tuni mutum 578 suka mutu.
Zai ci gaba da jan ragamar gwamnati na yaki da cutar. A farkon makon nan ne mai magana da yawun Mista Johnson ya ce idan firai ministan ya fara rashin lafiya har ma ya kasa aiki, to Sakataren Harkokin Wajen kasar Dominic Raab, ne wanda aka zaba ya tsaya a madadinsa.
Babu tabbas kan ko Mr Johnson zai ci gaba da zama da budurwarsa Carrie Symonds, wacce take da tsohon ciki.
An shawarci mata masu juna biyu da su zama masu tsantseni wajen bin matakan kariya kamar na bayar da tazara har na tsawon mako 12.
Wannan na zuwa ne bayan da Yariman Wales ma gwaji ya nuna ya kamu da cutar a farkon makon nan.
Yarima Charles mai shekara 71, ya dan nuna alamun cutar saisa-saisa, ''amma lafiyarsa lau ba ta yi muni ba,'' a cewar wani mai magana da yawunsa.












