Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Yan Najeriya 51 ne suka kamu da cutar'
Cibiyar takaita yaduwar cutuka a Najeriya ta tabbatar da samun karin mutum biyar da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.
Bayanan da cibiyar ta wallafa a shafinta na sada zumunta cikin daren Alhamis, na cewa biyu daga cikin mutanen a Babban birnin tarayya Abuja suke, sai biyu a jihar Legas, da kuma wani a jihar Rivers.
Da wadannan alkaluma, Rivers ta zama jiha ta baya-bayan nan da aka samu bullar cutar coronavirus ke nan a Najeriya.
Ta ce mutum uku daga cikinsu matafiya ne da suka dawo gida Najeriya yayin da biyun kuma sun yi hulda ne da masu dauke da cutar.
Zuwa yanzu dai, hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun mutum hamsin da daya wadanda annobar coronavirus ta kama.
A cikin wannan adadi kuma, biyu sun samu lafiya an sallame su, yayin da guda ya riga mu gidan gaskiya.
An shiga zullumi matuka ganin yadda cutar ta kama wasu manyan jami'an gwamnati a Najeriya ciki har da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad wanda aka tabbatar ya kamu da coronavirus bayan fitowar sakamakon gwajin da aka yi masa.
Haka shi ma, shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari ya kamu da cutar, inda yake can kwance yana jinya.
Har wa yau, wata majiya mai tushe a fadar gwamnatin ta Najeriya, ta tabbatarwa da BBC cewa " da gaske ne batun Abba Kyari ya kamu da coronavirus."
Kafin nan dai BBC ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu kan al'amarin amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.
Reuters dai ta rawaito cewa Abba Kyari ya yi bulaguro zuwa Jamus ne a farkon watan Maris tare da wasu jami'an gwamnatin kasar domin yin wani taro da kamfanin Siemens.