Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus : 'Yan Majalisar Najeriya na son a sassauta haraji
Majalisar wakilan Najeriya ta soma muhawara kan wani kuduri da zai regewa kamfanoni da dai-daikun mutane harajin da suke biya wajen shigo da kayayyaki cikin kasar.
Majalisar ta bijiro da wannan kudiri ne a wani mataki na rage kaifin matsalar tattalin arzikin da bazuwar cutar coronavirus ke haddasawa.
Kudurin mai suna Emergency Economic Stimulus Bill, zai yi kokarin kare wasu 'yan kasar da ke fuskantar barazanar rasa aikinsu sakamakon shawarar wasu kamfanonin na yi wuwar rage ma'aikata idan al'amarin ya kara tsananta.
Daya daga cikin 'yan majalisar daga jihar Jigawa, Hon. Ahmed S. Fulani, ya shaida wa BBC cewa kudirin ya kunshi dai na cirewa ma'aikata harajin gidaje na wucin-gadi, sai kayayyakin da ake shigo da su don inganta fanin lafiya.
Ya ce janye wadannan haraji musamman ga 'yan kasuwa ko kamfanoni za su bada damar shigo da kayayyaki a sawwake su kuma wadatar da al'aumma a fadin kasar.
Hon. Ahmed ya ce shi haraji yana tafiya dai-dai da yanayin samuwar mutum, don haka a wannan yanayin da ake ciki babu alfanun tsawwala haraji.
Ya ce ''Idan ta kama abin da ya shafi kasa da ci gabanta maganar guda ce, don haka muna da yakinin kudirin zai samu shiga da nasara don ciyar da kasarmu gaba''.
To sai dai tuni 'yan majalisar wakilan da takwarorinsu na dattawa suka dage yin zama har nan da makonni biyu saboda cutar Covid-19.
Shugaban Majalisar dattawan Ahmad Lawan ne ya bayyana haka bayan wani zama da majalisar ta a ranar Talata.
Zuwa yanzu mutum 44 aka gano masu dauke da cutar a Najeriya, ciki akwai gwamnan Bauchi da kuma shugaban ma'aikata na fadar gwamnati Abba Kyari.
Mutum guda annobar ta yi sanadiyar mutuwarsa a Najeriyar, akwai kuma biyu da suka warke.