Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wadanne bayanai ne kuke son sanin sahihancinsu kan coronavirus? Ku aiko da tambayoyinku
A yayin da ake ci gaba da samun yaduwar cutar coronavirus a fadin duniya, a lokacin ne kuma ake ta samun karuwar bayanan karya kan cutar a intanet.
Ko a makon da ya gabata mun nemi ku aiko tambayoyi kan cutar, a wannan makon kuma muna neman ku aiko da tambayoyinku ne kan bayanai ne da ake yadawa a intanet kan coronavirus da kuke son sanin sahihancinsu.
BBC kuma za ta gudanar da bincike tare da kawo muku cikakkiyar makala. Sai dai ku sani ba dukkan bayanan ba ne za mu iya nemo muku sahihancinsu, don abin da yawa.
Amma za mu zabi mafi muhimmanci mu yi binciken gaskiyarsu.
Ku sanya sunanku a kasa idan kuna son a wallafa tambayarku a cikin makalar.