Chelsea na son sayo Declan Rice

An wallafa

Chelsea na son sayo dan wasan West Ham da Ingila Declan Rice, mai shekara 21, a bazara. (Sky Sports)

Newcastle na fatan sayen dan wasan Ingila Danny Rose, mai shekara 29, wanda yake can a matsayin aro daga Tottenham idan aka sake bude kasuwar musayar 'yan wasa a bazara. (I Sport)

Arsenal na son dauko dan wasan Celtic dan Faransa Odsonne Edouard, mai shekara 22, a yunkurinsu na inganta kungiyar kafin kakar wasa mai zuwa. (Mirror)

Kocin Tottenham Jose Mourinho yana taimaka wa mutane a yayin da ake ci gaba da fama da coronavirus inda yake bai wa tsofaffin da ke zaune a kusa da filin wasan kungiyar abinci. (Football.London)

Manchester United ta samu kwarin gwiwa a kokarinta na sayo dan Birmingham Jude Bellingham a yayin da Borussia Dortmund ta janye janye aniyarta ta sayo dan wasan na Ingila mai shekara 16. (Mirror)

Dan wasan Bayern Munich da Austria David Alaba, mai shekara 27, ba zai karbi tayin da za a yi masa na komawa Manchester City a bazara ba, saboda yana son komawa ko dai Real Madrid ko kuma Barcelona. (Bild, via Sports Mole)

Dan wasan Lille dan kasar Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 21, ya zama dan wasan da Manchester United "za ta bai wa muhimmanci" idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa. (Le10 Sport, via Star)

Manchester City na sha'awar sayen dan wasan Brescia da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 19. (Corriere dello Sport, via Sport Witness)

Tottenham na son dauko dan wasan QPR dan kasar Ingila Eberechi Eze, mai shekara 21, yayin da rahotanni suka ce Crystal Palace da Sheffield United, wadanda su ma suke son sayensa, ba za su iya biyan QPR £20m a kan dan wasan ba. (Express)

Attajirin nan na Amurka Michael Dell, mai shekara 55, wanda aka ce yana da dukiyar da ta kai $31.2bn, yana duba yiwuwar zuba jari a Derby County.(NBC Sports)

Tsohon mamallakin kungiyar Leeds kuma shugaban Brescia Massimo Cellino, ya yi kira a soke gasar Serie A ta Italiya saboda "annobar" coronavirus. (Guardian)