Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona za ta dauko Laporte, Koulibaly zai bar Napoli
Barcelona na sha'awar dauko dan wasan Manchester City dan kasar Faransa Aymeric Laporte, mai shekara 25 a bazara. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Paris St-Germain, Real Madrid da kuma Manchester City na duba yiwuwar sayo dan wasan Inter Milan dan kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25 a bazarar da ke tafe. (Calciomercato - in Italian)
Kalidou Koulibaly, mai shekara 28, na shirin barin Napoli a bazara, a yayin da ake hasashen cewa dan kasar ta Senegal zai koma Manchester United. (Mirror)
Barcelona na son sayar da dan wasan Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 29, a kan for euro 100m a bazara - shekara daya bayan ta sayo shi daga Atletico Madrid a kan euro 120m. (Sport)
Liverpool da Arsenal sun sanya ido a kan dan wasan Eintracht Frankfurt dan kasar Faransa van Ndicka, mai shekara 20, kafin a dakatar da kakar wasa ta bana. (Sky Sports)
Arsenal na tattaunawa da likitocin sauran kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya a kan ko zai yiwu su koma atisaye a makon da muke ciki. (Mail)
Barcelona na tattaunawa da manyan 'yan wasanta domin rage albashinsu saboda kungiyar ba za ta iya biyan alawus dinsu wanda ya zarta euro 1bn har zuwa karshen kakar wasan bana ba. (Marca)
Dan wasan Juventus Gonzalo Higuain, mai shekara 32, ya keta dokokin killace kai a Italiya domin ya tafi kasarsa Argentina don ganawa da mahaifiyarsa wacce ke fama da cutar daji. (Sun)
Mahaifin dan wasan Real Madrid Luka Jovic ya ce dole dan nasa ya amince da hukuncin da za a yanke masa - ko da kuwa ya hada da hukuncin zaman gidan yari - saboda ya keta dokar killace kai inda ya kai ziyara wurin budurwarsa a Belgrade. (Marca)
Tsohon dan wasan Arsenal da Barcelona Alexander Hleb ya ce "babu wanda ya damu" da cutar coronavirus a kasarsa Belarus, kasa ta karshe da har yanzu ake buga gasar kwallon kafa. (Sun)