Liverpool za ta sabunta kwangilar Alisson, Ancelotti na son sayo Ciro

An wallafa

Golan Brazil Alisson, mai shekara 27, da dan wasan Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 28, na dab da sanya hannu a sabon kwantaragi a Liverpool. (Goal)

Dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho zai zama wata "babbar karuwa" ga tawagar Chelsea, a cewar tsohon kyaftin din kungiyar John Terry, amma rahotanni sun ce kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer yana son dauko dan wasan dan kasar Ingila mai shekara 19. (Evening Standard)

Hukumar Gasar Firimiya tana yin wani shiri na kwarya ta bi kwarya domin a soma gasar ranar daya ga watan Yuni, ta yadda za a kammala kakar wasan cikin mako shida sannan a soma kakar wasa ta 2020-21 ranar takwas ga watan Agusta. (Telegraph)

Kocin Everton Carlo Ancelotti yana son sayo dan wasan Lazio dan Italiya Ciro Immobile mai shekara 30. (Goal)

Wakilan dan wasan Paris-St-Germain Neymar, mai shekara 28, sun shaida wa Barcelona cewa dan wasan dan kasar Brazil yana son barin kungiyar domin ya koma Nou Camp. (Star)

An nemi Arsenal ta sayo dan wasan Burnley dan kasar New Zealand Chris Wood, mai shekara 28, domin maye gurbin Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, idan dan kasar ta Gabon ya zabi barin kungiyar a bazara. (Star)

Ana rade radin cewa Manchester United na shirin kashe £50m domin sayo Aubameyang, a yayin da Inter Milan da Barcelona ke zawarcinsa. (Metro)

Dakatarwar da aka yi wa kungiyoyin kwallon kafa daga buga wasa saboda coronavirus zai iya bai wa Paris St-Germain karin lokaci na rarrashin dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, don ya sanya hannu a sabon kwantaragi a yayin da kwangilarsa za ta kare a 2022. (Marca)

Manchester United ta tattauna da dan wasan Atletico Madrid dan kasar Faransa Thomas Lemar, mai shekara 24, wanda a baya Liverpool ke son daukarsa. (Manchester Evening News)