Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aymeric Laporte zai yi jinyar 'wata daya' - Pep Guardiola
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ana tsammani dan wasan bayan kungiyar Aymeric Laporte zai yi jinyar wata guda sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa.
An fitar da Laporte, mai shekara 25, daga cikin fili kafin a tafi hutun rabin lokaci a karawar gasar Zakarun Turai da suka yi da Real Madrid ranar Laraba - bayan da ya fito sau takwas kacal a kakar wasa ta bana.
"Ya ji rauni a cinyarsa. Zai yi jinyar mako uku ko kasa da haka - ko kuma wata daya," in ji Guardiola ranar Juma'a.
"Abin takaicin shi ne wannan lamari ya faru ne bayan ya kashe wata hudu zuwa biyar bai buga tamaula ba."
Laporte ya koma buga tamaula ne a wasan da City ta doke Sheffield United da ci 1-0 a gasar Firimiya a watan Janairu, bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa a watan Agustan 2019.
Bayan wasan, Guardiola ya ce dawo da dan wasan zai zama tamkar ganganci, ko da yake ya bayyana dan kasar ta Faransa a matsayin "dan wasan baya mafi inganci a duniya".
Laporte, wanda ya buga wasansa na hudu tun da ya dawo daga jinya, an maye gurbinsa da Fernandinho bayan minti 33 a Madrid.
"Rayuwa na da matukar wahala kuma wadanda suke jure mata su ne mutanen da suka fuskanci kalubale," a cewar Guardiola.