Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An rufe makarantun Islamiyya da na Allo a Jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe makarantun Islamiyya da kuma tsangayu (makarantun allo) a jihar domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Shugaban makarantun Islamiyya da tsangayu na Jihar Kano, Gwani Yahuza Dan Zarga ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ya ce an dauki matakin ne domin kauce wa yaduwar cutar coronavirus.
"Kwamishinan ilimi ya yi taron manema labarai ya fada sannan kuma ya kara yi mani gargadi cewa na fada wa masu makarantu da su bi wannan doka ta gwamnati," in ji Gwani Yahuza.
Ya kara da cewa: "An dauki matakin ne domin kare lafiyarsu sannan kuma matakin ya shafi dukkanin makarantun Islamiyya da na tsangaya."
Gwani ya ce daga gobe Litinin ne matakin zai fara aiki, sannan kuma ya yi kira ga malamai da masu makarantun da su dukufa da addu'o'i da niyyar Allah ya kawo karshen cutar ta Covid-19.
Mutum 30 ne jumulla suka kamu da coronavirus a Najeriya kuma Jihar Kano ba ta cikin jihohin da cutar ta bulla.
Jihohin da aka samu Covid-19 a Najeriya
Legas - 22
Abuja - 4
Ogun - 2
Ekiti - 1
Oyo - 1
Jumulla - 30
Wadanda suka warke - 2