Coronavirus: 'Covid-19 ba ta bulla a Jami'ar Bayero ta Kano ba'

An wallafa

Hukumar Jami'ar Bayero ta Kano ta ce ba gaskiya ba ne labarin da aka rika yadawa cewa an samu bullar cutar Covid-19 (coronavirus) a jami'ar.

Da tsakar ranar yau Lahadi ne dai aka fara yada wani labari da ke cewa Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da wasu dalibai biyu sun kamu da Covid-19 a Jami'ar Bayero.

Wani shafin intanet ne da ke dauke da sunan sashen Ingilishi na BBC ya wallafa labarin, wanda aka rika yadawa a shafukan sada zumunta.

A cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Shugaban Jami'ar, Farfesa Muhammad Yahuza ya ce labarin na kanzon kurege ne sannan ya ce babu ma dalibai a dakunan kwanan jami'ar.

Kazalika ba kafar yada labarai ta BBC ce ta wallafa labarin ba - shafin boge ne.

"Wannan labari ba shi da tushe ballanta makama," in ji Farfesa Yahuza.

Ya ci gaba da cewa: "An dauki hoton boge ne na shafi mai sunan BBC ana yadawa domin a nuna kamar daga BBC yake.

"A halin yanzu ma babu dalibai a dakin kwana na Jami'ar Bayero. Kamar yadda aka sani an yi yajin aiki na sati biyu. Kafin haka kuma dalibanmu suna hutun tsakiyar zango. Mun bayar da hutun mako daya sai kuma aka tafi yajin aikin."

Farfesa Yahuza ya kuma yi Allah-wadai da wadanda suka kirkiri labarin karyar sannan ya yi kira ga masu yadawa da su guji yin hakan.

Zuwa lokacin wallafa wannan labarin, hukumomi a Najeriya ba su bayyana batun bullar cutar coronavirus ba a arewacin kasar ban da mutum hudu a Abuja.

A rahoton da hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka ta fitar ranar Lahadi, mutum 30 ne suka kamu da Covid-19 a Najeriya - 22 daga cikinsu a Jihar Legas suke.

Jihohin da aka samu Covid-19 a Najeriya

  • Legas - 22
  • Abuja - 4
  • Ogun - 2
  • Ekiti - 1
  • Oyo - 1
  • Jumulla - 30
  • Wadanda suka warke - 2