Coronavirus: Mutum 35 ne suka kamu a Nigeria

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar da ke hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fito da jerin alkaluman mutanen da annobar coronavirus ta kama a jihohin kasar.

Bisa alkaluman hukumar, ya zuwa yanzu Litinin 23 ga watan Maris, 2020 za a iya cewa ban da birnin Abuja, dukkannin mutanen da cutar ta kama sun fito daga kudancin kasar ne.

Jihohin da aka samu Covid-19 a Najeriya:

  • Legas- 25
  • Abuja- 6
  • Ogun- 2
  • Ekiti- 1
  • Oyo- 1
  • Edo- 1

Haka kuma, hukumar ta sanar da mutuwar mutum daya- wani mai shekaru 67- wanda ya dawo daga Burtaniya.

NCDC, ta shawarci duk wanda ya san ya dawo kasar daga ketare a makonni biyu da suka gabata da ya killace kansa.

Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 30 inda aka sallami mutum biyu daga cikinsu bayan sun warke.

A Jamhuriyar Nijar kuwa, an kara samun mutum na 2 da ke dauke da coronavirus.

Mutumin dai dan kasar Italiya ne da ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta a kasar.

Hukumomi a kasar sun ce mutumin ya shiga kasar ne tun a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata amma bai nuna alamar cutar ba sai a ranar Asabar.

Wannan ne dai karo na biyu da aka samu wani mai dauke da coronavirus a Nijar, mutumin na da shekaru sama da hamsin a duniya kuma ya je kasar ne sama da mako biyu daga Italiya.

Ministan lafiya na kasar Dakta Idi Mai Nasara ya shaida wa BBC cewa, tuni aka garzaya da mutumin zuwa asibiti inda ya ke karbar magani, kuma tuni aka killace wasu mutum saba'in da shida da suka yi mu'amala da mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar.

Sannan, an kuma killace wasu mutum uku da suka fito daga Italiya inji ministan lafiyar.

Sakamakon binciken da aka gudanar akan wasu mutane 26 da ake kiyautata zaton cewa suna dauke da cutar corona, an tabbatar da 16 daga cikin na dauke da cutar a Kamaru.

Hakan ya kaiga a yanzu mutane 56 ne suka kamu da cutar tun daga ranar 6 ga watan maris, ranar da aka gano mutum na farko (wani bafaranshe) da ya kamu da cutar.

A yanzu dai wannan cutar ta bazu ne a manyan birane 3 na Kamaru da suka hada da Yaoundé cibiyar gwamnati, da Douala cibiyar harkokin kasuwanci da Bafoussam babban birni na uku a kasar.

Duk da cewa kusan mako guda kenan da Hukumomi suka dauki wasu matakai na yunkurin dakile bazuwar cutar Corona, amma kuma bisa ga dukkan alamu adadin mutanen da suka kamu da cutar na ta yawaita kusan a ko wace rana.

A wani labarin kuma, an samu mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar coronavirus a Ghana.

Sannan a wani mataki na dakile yaduwar cutar a kasar wadda a yanzu haka akwai mutum fiye da 20 da suka kamu, daga ranar Lahadi ne za a rufe iyakokin kasar zuwa nan da makonni biyu, sannan kuma za a rinka killace duk wasu baki da zarar sun isa kasar.

Haka Uganda ma ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar.

Mutumin dai dan kasar ne wanda ya dawo daga Dubai.

Shugaban kasar Yoweri Museveni, ya sanar da cewa daga ranar Lahadi za a dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na fasinja sannan za a takaita dukkan tafiye-tafiye ta sama da ta kasa har ma da ta ruwa a wani mataki na dakile yaduwar cutar.

Uganda dai ita ce kasar Afirka ta baya-bayan nan da aka samu bullar cutar coronavirus.