Coronavirus: Direbobi sun bukaci a waiwaye su

Asalin hoton, Getty Images
Babbar kungiyar sufiri ta Najeriya, RTEAN ta roki gwamnatin kasar ta taimaka mata wajen hana yaduwar annobar coronavirus tsakanin fasinjoji da direbobinta a tashoshin motar haya.
Shugaban kungiyar na kasa Dakta Muhammad Musa Maitakobi, ya ce yanzu haka akwai abubuwan da suke yi na kariya, sai dai ba su wadatar ba, domin akwai bukatar gwamnatocin jihohi da na tarayya su taimaka musu.
Dakta Muhamamad, ya shaida wa BBC cewa sun dukufa wajen daukar matakai da fadakar da mambobinsu game da illar Covid-19.
Ya ce ''Na shaida wa shugabanninmu na jihohi su tanadi wajen wanke hannu na direbobi da fasinja, sannan duk fasinjoji a matsa musu sinadarin tsaftacce hannu kafin su shiga mota.''
Sai dai ya ce suna fuskantar kalubale domin ba su da na'urar da ake auna zafin jiki.
Ya ce, '' Muna bukatar taimakon na'urar da ke auna zafin jiki da tantance ko mutum yana dauke da wannan cuta, ba mu san inda ake sayarwa ba, muna da yara a kowanne gareji da za a iya koyawa yadda ake amfani da na'urar''.
Gwamnatin Najeriya dai na ta sanar da matakai da suka hada da hana jiragen sama daga kasashen waje sauka a dukkanin filayen jiragen saman kasar sakamakon yakin da ake yi na dakile cutar Covid-19.

Asalin hoton, Getty Images
Kazalika an dauki matakan bincike da kuma hana taruka tare da umartar manyan katunan su tsaurara matakai.
Sai dai da alama wadannan matakai ba su shafi tashoshin motocin haya ba inda nan ne galibi marassa karfi da akasari al'umma ke shiga mota.
Wannan dalili ne a cewar Dakta Muhammad ya sanya kungiyarsa ta yunkuro gadan-gadan domin tabbatar da an lalubo duk wasu hanyoyi da za a kare lafiyar matafiya a tashoshinsu.
Sannan sun kuma dukufa wajen wayar da manya da kananan direbobi da kuma fasinjoji a game da hadarin da ke tattare da cutar mai sarke numfashi.
Yanzu haka dai mutum 22 aka tabbatar na dauke da Covid-19 a Najeriya, biyu sun warke.












