Kotun Koli ta saurari batun zaben APC a Zamfara

Abdula'azirz Yari
Bayanan hoto, Abdula'azirz Yari ya mulki jihar tsawon shekara takwas daga 2011 zuwa 2019
An wallafa

Kotun Koli ta Najeriya ta saurari bahasi daga bangarori biyu na jam'iyar APC na jihar Zamfara game da sake duba hukunci da kotun ta yanke kan yadda zaben fitar da gwani na gwamna ya gudana a jihar a bara.

Wani bangare na jam'iyyar APC ne ya nemi kotun ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke da ya nuna cewa APC ba ta da dan takara a jihar ta Zamfara saboda ba ta yi zaben fitar da gwani yadda ya dace ba.

Hukuncin kotun na lokacin dai ya sa jam'iyyar PDP ta tsinci dami a kala, inda dan takararta na gwamna Bello Matawalle ya zama gwamnan jihar, duk da ba shi ne ya lashe zaben gwamna ba.

Wasu 'yan APC din a jihar ta Zamfara karkashin Sanata Kabiru Marafa ne ya kai kara kotu yana neman a yanke hukunci kan ko APC ta yi halattaccen zabe a jihar ko kuwa.

Bangaren tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari ne ya nemi kotun ta Koli ta sake nazari kan hukuncin, wanda bai yi musu dadi ba.

Bayan sauraren bangarorin biyu a ranar Talata, kotun ta sanar da cewa a gaba za ta tuntubi bangarorin biyu domin sanar da su ranar da za ta yane hukunci.

Lauyoyin masu shigar da kara dai sun sun ce ba wai " muna kalubalantar hukuncin kotun ba ne, amma muna so a sake duba shi ne don kada ya warware wasu hukunce-hukuncen kotun ta koli sama da 20,000," a cewar Robert Cleck daya daga bangaren lauyoyin bangaren Abdul-aziz Yari.

To amma su kuwa lauyoyin bangaren masu kariya wato Sanata Kabiru Marafa suna ganin in har ana so kotun ta warware hukuncin na ta, to sai dai a gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashin da ya bai wa Kotun Koli karfin iko kan hukuncin da ta yanke ya zauna har abada. Da kuma gyra ga sashen da ya ce shari'ar zabe na da wa'adin kwanaki 60 ne kawai bayan zaben,'' kamar yadda Barista Mike Ozekome ya shaida wa BBC

Nan gaba ne dai kotun za ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan wannan bukata.