Dalilan dakatar da wasu sarakuna a Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle

Asalin hoton, Bellomatawalle1

Bayanan hoto, Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle
An wallafa

Gwamnatin jahar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da dalilan da ta ce yasa ta dakatar da wasu sarakunan gargajiya biyu.

Kwanaki biyu da suka wuce gwamnatin ta hannun mai bai wa gwamna shawara akan lamurranta na sarautu ta sanar da dakatar da uwayen kasar Bakura da Zurmi.

A farkon makon nan ne gwamnatin ta sanar da dakatar da Alhaji Bello Garba Kanwa, Sarkin Yakin Kanwa da kuma da kuma Alhaji Muhammad Bello Yusuf wanda shi ne Marafan Bakura ba tare da sanar da dalili ba.

To amma a ranar Talata wata sabuwar sanarwa ta hannun mai ba da shawara kan lamuran sarautun Alhaji Yusuf Abubakar Zugu, na cewa an dakatar da uwayen kasar biyu ne bisa rashin biyayya da kuma karan tsaye ga shirye-shiryen gwamnati.

Sauran laifukan sun hada da shiga dumu-dumu cikin harkokin siyasa da kuma zargin almundahana da ruf da da ciki da dukiyar al'umma da take yi wa uban kasar Kanwa Alhaji Bello Garba.

To amma da yawa na ganin takun saka tsakanin sarakunan da kuma gwamnatin jihar ba ya rasa nasaba da siyasa.

Kuma wannan ya fara tun lokacin da uwayen kasar suka karbi belin wasu tsoffin kwamishinoni a bangaren jam'iyyar adawa ta APC da gwamnatin Bello Matawalle ta tsare bisa wasu zarge-zarge.

A hira da BBC a farkon mako Yusuf Abubakar Zugu ya musanta cewa akwai siyasa cikin dakatar da sarakunan.

Jam'iyyar adawa ta APC ko a baya ta fitar da sanarwar cewa 'ya'yanta a jihar Zamfara na fuskantar takura daga gwamnatin PDP mai ci, wani abu da gwamnatin ke musantawa.

Wannan ba shi ne karon farko da Gwamna Bello Matawalle ya dakatar da sarkin gargajiya ba, a kokarin yin garambawul kan mastalar tsaro da jihar ke fama da ita.

To sai dai a wannan karon wasu na zargin cewa akwai lauje cikin nadi.